'Ba za mu daina shiga Abuja ba har sai an saki El-zakzaky'

Asalin hoton, Getty Images
Mabiya mazhabar Shi'a karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim El-zakzaky sun ce ba za su daina gudanar da zanga-zanga a birnin Abuja ba har sai idan an saki jagoransu da ke tsare tun 2015.
Wannan dai martani ga sanarwar da mai magana da yawun Shugaban Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya fitar ranar Juma'a, inda ya nemi 'yan kungiyar ta Islamic Movement of Nigeria su daina hawa titunan birnin kasar suna 'tayar da zaune tsaye'.
Sanarwar dai ta kara da cewa "bai kamata a rinka dora wa Shugaba Buhari laifin ci gaba da rike jagoran kungiyar Islamic Movement of Nigeria, Sheikh Ibrahim El-zakzaky ba."
Mai magana da yawun shugaban ya ce, kasancewar batun jagoran na IMN na gaban kotu a jihar Kaduna, "bai kamata a zargi gwamnatin tarayya da ci gaba da rike shugaban mabiya mazhabar Shi'a, Ibrahim El-zakzaky ba."
Malam Garba Shehu ya kara da cewa "fadar gwamnatin Najeriya na jan hankalin mabiya mazhabar ta Shi'a da su jira hukuncin da kotun Kaduna inda aka gurfanar da Sheikh Zakzaky za ta yanke, maimakon tayar da zaune tsaye."
Sanarwar ta kara da cewa "ko kadan bai dace ba a rinka tayar da yamutsi alhali batun da ake magana a kai yana gaban kuliya."
Garba Shehu ya yi gargadi cewa "gwamnati ba za ta zuba ido tana ganin ana hawa tituna ana karya dokokin kasa ba kamar yadda babu wata kasa da za ta jure hakan."
Har wa yau, sanarwar ta sake jan hankalin 'yan Shi'ar da su "daina hawa tituna suna ambato sunan Buhari suna zagi tare da yi masa fatan mutuwa."

Asalin hoton, Twitter

Martanin mabiya Zakzaky
Tun bayan wannan sanarwa da gwamnatin Najeriya ta fitar, magoya bayan jagoran na IMN, Sheikh Ibrahim El-zakzaky, suke ta bayyana ra'ayoyinsu.
BBC ta ji ta bakin Ahmed Bawa Jalam kan wannan sanarwa, inda ya ce "mu kam a kan jagoranmu babu gudu babu ja da baya."
Ya ce "idan har gwamnati na son mu daina hawa tituna muna zanga-zanga to sai ta sakar mana jagoranmu wanda yake cikin halin tsananin rashin lafiya."
Ahmed Jalam ya kara da cewa "sanarwar ma ta kara nuna mana cewa muzaharar da muke yi na ci wa gwamnatin tuwo a kwarya saboda haka muna kira ga sauran 'yan uwa da su ci gaba da muzahara a Abuja, har sai lokacin da aka sakar mana malam."

Asalin hoton, Getty Images

Me ya janyo sanarwar?
Mabiya mazhabar Shi'a dai sun ci gaba da gudanar da jerin zanga-zangar neman gwamnati ta saki jagoran nasu ta mai dakinsa wadanda suke tsare tun watan Disambar 2015, bayan sojoji sun far wa 'yan kungiyar a Zariya, bisa zargin rufe hanyar hafsan sojin kasar, Laftanar Janar Tukur Burutai.
Ko a ranar Juma'ar nan sai da mabiya El-zakzaky suka yi zanga-zanga a Abuja, babban birnin kasar, duk da dokar da rundunar 'yan sanda ta kafa na hana zanga-zanga a wani wuri a birni ba dandalin Unity Fountain ba da ke tsakiyar Abuja.
'Yan kungiyar ta IMN dai na nuna damuwa ne dangane da 'tsananin rashin lafiya' da suka ce jagoran nasu na fama da ita.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne Sheikh Zakzaky da maidakinsa suka sake bayyana a gaban kotun Kaduna da ke shari'ar, amma kuma ba su samu belin da suke nema ba na neman samun damar fita kasar waje domin samun lafiya.
Kotun ta dage karar ne har zuwa ranar 29 ga watan Yulin nan.
'Yan Shi'ar dai na yawan yin nuni da hukuncin da wata babbar kotu a Abuja ta yanke a 2016, inda ta bayar da umarni a saki El-zakzaky da matarsa sannan a biya su diya tare da gina musu muhalli a duk inda suke bukata.










