Yadda Aljeriya ta lashe kofin AFCON

Labarai da bayanai kai-tsaye game da wasan karshe a Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka AFCON 2019.

Rahoto kai-tsaye

Umar Rayyan and Umar Mikail

  1. Sai wani lokacin, Aljeriya ta lashe kofin Afirka karo na biyu

    A za muka kawo karshen kawo bayanai da sharhi kan wasan karshe na lashe kofin Afirka.

    Muna yi wa magoya bayan Aljeriya murna, tare da taya magoya bayan Senegal bakin ciki.

    Sai wani lokacin.

  2. Yadda Aljeriya ta daga Kofin Afirka, Aljeriya ta lashe kofin Afirka karo na biyu

    Algeria

    Asalin hoton, Reuters

    Algeria

    Asalin hoton, Reuters

    Algeria

    Asalin hoton, Reuters

  3. Yadda Senegal ke jimami, Senegal 0-1 Aljeriya

    Senegal

    Asalin hoton, Getty Images

    Senegal

    Asalin hoton, Getty Images

    Senegal

    Asalin hoton, Getty Images

    Senegal

    Asalin hoton, Getty Images

  4. Aljeriya ce zakarar Afirka, Senegal 0-1 Aljeriya

    'Yan wasan Aljeriya

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan wasan Aljeriya

    Asalin hoton, Getty Images

  5. Aljeriya ce zakarar Afirka, Senegal 1-0 Aljeriya

    Wannan nasara ba karama ba ce ga Riyad Mahrez, wanda dama tuni ya lashe kofin Firimiyar Ingila tare da Man City.

    Yanzu matsayinsa zai kara sama a harkar kwallon kafa.

    Shi ne gwarzon dan kwallon kafar Afirka na BBC a 2016 da kuma CAF

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    A

    Asalin hoton, Getty Images

  6. Ajeriya ce zakarar Afirka, Senegal 0-1 Aljeriya

    Magoya bayan Aljeriya kenan suna murna a birnin Marsel na kasar Faransa

    Magoya bayan Aljeriya a Faransa

    Asalin hoton, Getty Images

  7. Yadda wasan ya kasance, Senegal 0-1 Aljeriya

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  8. An tashi wasa, Senegal 0-1 Aljeriya

    Aljeriya ta sake lashe kofin kasashen Afirka.

    Wannan shi ne karo na biyu da suke daga kofin. Sun dauki na farko a shekrar 1990, bayan shekara 29 ga shi sun dauki na biyu.

    Aljeriya

    Asalin hoton, Getty Images

  9. An ba Mandi katin gargadi, Senegal 0-1 Aljeriya

    Alkalin wasa ya ba Mandi katin gargadi.

  10. Senegal 0-1 Aljeriya, Senegal 0-1 Aljeriya

    Aljeriya na dab da daukar kofin Afirka a karo na biyu cikin shekara 62 da aka fara gasar. Rabonsu da kofin tun a shekarar 1990, shekara 29 kenan

  11. An kara minti hudu, Senegal 0-1 Aljeriya

    Alkalin wasa ya kara minti hudu.

  12. Senegal 0-1 Aljeriya, Senegal 0-1 Aljeriya

    Islam Silaimani ya karbi Baghdad Bounedjah na Aljeriya

  13. An yi wa Keita keta, Senegal 0-1 Aljeriya

    An yi wa Keita na Senegal keta, amma an yi bugun tazara kwallon ta fita.

  14. Tahrat ya canja Feghouli, Senegal 0-1 Aljeriya

    Tahrat na Aljeriya ya canja Feghouli.

  15. Mummunan hari, Senegal 0-1 Aljeriya

    Ismaila Sarr na Senegal ya zubar da kwallo mai kyan gaske.

    A cikin yadi na 18 ya harba kwallo sama bayan ya gama kintsawa kafin ta diro daga sama, amma ya harba ta saman raga a minti na 83

  16. Senegal 0-1 Aljeriya, Senegal 0-1 Aljeriya

    An bai wa Gassama na Senegal katin gargdi, kuma shi ne na biyu da aka ba su.

  17. Minti na 79, Senegal 0-1 Aljeriya

    Hankalin Aljeriya ba a kwance yake ba a wannan wasa, sun ci amma ba su huta ba, sannan kuma babu alamun za su kara kwallo ta biyu

  18. Benlamri ya ji rauni, Senegal 1-0 Aljeriya

    Djamel Benlamri na Aljeriya ya ji rauni a fuskarsa, ya fita wajen fili don neman magani.

  19. Minti na 75, Senegal 0-1 Aljeriya

    Mbaye Diagne ya canji Henry Saivet na Senegal

  20. Aljeriya ta samu bugun kwana, Senegal 0-1 Aljeriya

    Aljeriya ta samu bugun kwana, amma Senegal ta cire kwallon.