Me ya rage wa Super Eagles bayan Rasha?

Lionel Messi na Argentina da kuma Mikel Obi na Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Lionel Messi ne ya jagoranci Argentina ta doke Najeriya, abin da ya fitar da ita daga gasar
    • Marubuci, Aliyu Tanko
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, daga St Petersburg
  • An wallafa

Burin tawagar 'yan kwallon Najeriya a gasar cin kofin duniya ya kawo karshe ne sakamakon rashin nasarar da suka fuskanta a karawarsu da Argentina a wasansu na karshe na zagayen farko a ranar Talata.

Murnar 'yan Najeriya ta koma ciki ne bayan da Argentina ta doke su da ci 2-1 musamman kwallo ta biyu da aka sha Super Eagles din 'yan mintuna kafin a tashi wasa a birnin St Petersburg.

Abin da masu sha'awar kwallon kafa ke tambaya shi ne to me ya rage wa Najeriya ko kuma makomar tawagar?

Rike Gernot Rohr

Ci gaba da barin kocin Najeriya Gernot Rohr domin ya ja ragamar Super Eagles zai taimaki tawagar wajen kara bunkasa harkar kwallon 'yan wasan kasar.

A cikin watan Nuwambar bara ne ya sabunta kwangilarsa da Najeriya kuma duk da cewa kasar ba ta wuce zagayen farko a gasar cin kofin duniya ba, akwai bukatar a kara bashi dama.

Musamman saboda ganin akwai wasannin da ke tafe wadanda za su fayyace ko kasar za ta halarci gasar cin kofin kwallon Afirka watau AFCON a kasar Kamaru a badi.

Barin Bajamushe Rohr a kujerarsa zai tabbatar da daidaito a Super Eagles.

Kuma hakan zai ba shi damar nazari a kan kura-kuran da aka yi a baya domin gyara a nan gaba.

Tsarin horas da matasa

Tawagar Najeriya ita ce mafi karancin shekaru a gasar cin kofin duniya ta bana, abin da ke nuna cewa matasan kasar idan suka ci gaba da samun horo da kuma kwarin gwiwa za su kara gogewa kafin su tunkari wasu manyan wasannin da ke tafe a nan gaba.

Victor Moses

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Victor Moses na cikin kwararrun 'yan wasan Super Eagles, kuma ana ganin zai iya cigaba da taka rawa nan gaba

Fitar da tsari na musamman domin karfafawa matasan gwiwa tamkar shiryawa gaba ne a saboda haka ne kasar ke bukatar wannan tsarin.

NFF ta rike girmanta

Hukumar da ke kula da kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ita ce ke da alhakin tabbatar da walwalar 'yan kwallon da kuma gudanar da harkar a koda yaushe.

Yin aiki yadda ya kamata tare da samar da kakkawan yanayin da 'yan wasa za su bunkasa shi ne babban nauyin da ya kamata su sauke.

Albashin masu horaswa

A shekarun baya an samu 'yan matsaloli wajen biyan albashin masu horas da 'yan kwallon abin da ke janyo matsaloli wajen gudanar da harkokin yau da kullum.

'Yan wasan Super Eagles

Asalin hoton, PIUS UTOMI EKPEI

Bayanan hoto, Tawagar Najeriya ita ce mafi karancin shekaru a gasar cin kofin duniya ta bana

Akwai bukatar a dinga biyan hakkinsu a kan lokaci domin su ma su bada gudunmuwa dari bisa dari.

Samun nasarar 'yan kwallo na da alaka da yanayin da mai horas da shi ya ke ciki.

Ci gaban Najeriya a fagen kwallon kafa na bukatar sauke nauyi da cika alkawarin yarjejeniyar da aka kulla da masu horas da 'yan wasa.