Najeriya da Argentina: Anya laifin alkalin wasa ne?

Najeriya

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto, Na'urar da ke taimakawa lafari ce ta yanke hukuncin cewa kwallon da Marcos Rojo ya taba ba fanareti ba ne
An wallafa

Wadansu 'yan Najeriya suna ci gaba da dora laifi kan alkalin wasan da ya yi alkalanci a wasan da Argentina ta fitar da kasar daga gasar cin kofin duniya wadda ake yi a Rasha.

Argentina ta doke kasar ne da ci 2-1 a ranar Talata, abin da ya sa kasar ta kasa tsallake zuwa mataki na gaba a gasar.

Lionel Messi ne ya fara zura kwallo a ragar Najeriya a minti na 14, kafin Victor Moses ya farke kwallo bayan dawo daga hutun rabin lokaci da bugun fanareti.

Sai dai an samu ce-ce-ku-ce lokacin da kwallo ta taba hannun dan wasan Argentina Marcos Rojo a dari'ar gidansu.

Lamarin da ya sa wasu a shafukan sada zumunta ke cewa "an ba lafarin kudi", amma babu wata hujja da ta tabbatar da hakan.

'Yan wasan Najeriya sun rika korafi, abin da ya sa alkalin wasa Cuneyt Cakir, dan kasar Turkiyya, ya tsayar da wasan, inda ya kara kallon abin da ya faru a bidiyo.

Sai dai alkalin wasan ya ki amincewa ya ba Najeriya bugun fanareti, inda aka ci gaba da wasa kasashen biyu suna kunnen doki wato 1-1.

Cuneyt Cakir

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Alkalin wasa Cuneyt Cakir na kasar Turkiyya yana ci gaba da shan suka musamman a kafofin sada zumunta

Ana saura minti hudu a tashi wasa ne Rojo ya samu nasarar jefa wa Najeriya kwallo a raga, inda aka tashi wasa 2-1.

Jama'a sun rika bayyana ra'ayoyinsu a Najeriya game da bugun fanaretin na biyu da suke ganin ya kamata alkalin wasan ya ba kasar, inda wadansu ke ganin cewa shi ne dalilin da ya sa aka fitar da kasar.

BBC ta samu ra'ayoyi daga wadansu masu bibiyanmu a Facebook bayan mun wallafa labarin fidda Najeriya daga gasar.

Tama Muhammed cewa ya yi: "Gaskiyar magana shi ne alkalin wasa ne ya cire Najeriya daga gasar cin kofin duniya, ba kowa ba."

"Ya kamata Najeriya ta kai alkalin wasan nan kotu. Domin muna ji muna gani alkalin ya sa an ci mu saboda ya danne mana fanareti," in ji Abba Sa'ad Mahuta.

Haka dai ake ci gaba da tafka muhawa game da hukuncin da alkalin wasan ya yanke.

Cikin masu muhawara akwai wadansu da ke kwatanta abin da ya faru da bugun fanaretin da aka bai wa kasar Portugal a wasansu da Iran.

Portugal da Iran

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto, An rika yada wannan hoton a shafukan sada zumunta a Najeriya

Hakazalika akwai wadanda suke zargin alkalin wasan da karbar na-goro, kamar yadda suka wallafa wani hoton bogi da ke ikirarin nuna yadda aka yi wa wani alkalin wasa tayin ba shi kudi yayin da yake kallon bidiyon wani abu da ya faru a wani wasa.

Wani alkalin wasa

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto, Wani hoton bogi da aka rika yada wa a shafukan sada zumunta

Sai dai babu wata hujja da ta nuna ko tabbatar da zargin da aka wallafa a wannan hoto, hasalima hoton na boge ne.

Amma wani alkalin wasa dan Najeriya Ibrahim Musa ya kare hukuncin da lafarin ya yanke na kin bai wa kasar fanareti.

"Kullum shi alkalin wasa yana yin hukunci kuma yana duba niyyar dan wasa. Shin niyyar dan wasa ta ya aikata laifi ce. Ko niyyarsa ta ya buga kwallon ce.

To idan ka duba abin da ya faru kwallo ta taba hannun Rojo, hukuncin da alkalin wasa ya yanke ya yi daidai," kamar yadda Ibrahim ya shaida wa BBC.

facebook

Asalin hoton, Facebook