Watakila Neymar ya buga wa Brazil wasa da Koriya ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images
Watakila Neymar ya buga wasan da Brazil za ta fafata da Koriya ta Kudu ranar Litinin a karawar zagaye na biyu a Gasar Cin Kofin Duniya a Qatar.
Mai shekara 30 bai yi wa Brazil wasan da ta ci Switzerland ba da wanda Kamaru ta yi nasara a fafatawar cikin rukuni na bakwai.
Dan kwallon mai taka leda a Paris St Germain ya ji rauni a wasan farko a cikin rukuni da Brazil ta ci Serbia 2-0.
Brazil wadda ake sa ran za ta iya daukar kofin Qatar ta kai zaga na biyu tun kan ta fuskanci Kamaru a wasan karshe a rukuni na bakwai.
Koriya ta Kudu kuwa ta yi ta biyu ne a rukuni na takwas da maki hudu.
Wannan shi ne wasa na takwas da za a kece raini tsakanin tawagogin biyu, amma na farko a babbar Gasar tamaula ta Duniya.
Brazil ta yi nasara a wasa shida aka doke ta karawa daya - wasan karshe da suka fuskanci juna shi ne a watan Yuni, inda Brazil ta ci 5-1.
Duk wadda ta yi nasara a wasan Litinin za ta buga daf da na kusa da na karshe tsakanin Japan da Croatia.
Croatia ita ta yi ta biyu a Gasar Kofin Duniya da aka yi a Rasha a 2018, wanda Faransa ta lashe.











