Man City da Wolves sun cimma matsaya kan Nunes

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta cimma yarjejeniyar fatar baki da Wolves a cinikin dan wasan tsakiya Matheus Nunes kan kudi fam miliyan 47.3.
Wolves dai ta yi watsi da tayin da City ta yi a baya kan dan wasan na Portugal a makon da ya gabata, inda Wolves ta dage kan cewa tana son sama da fan miliyan 60.
Nunes bai halarci atisaye ba cikin kwanakin nan inda ya bayyana cewa yana son ya koma kungiyar Pep Guardiola.
Bugu da kari, Wolves ta amince da daukar dan wasan City na Ingila na kasa da shekara 21 Tommy Doyle a matsayin aro, tare da zabin siyan fam miliyan 4.3.
Wadannan yarjejeniyoyin biyu ba su da alaka da juna kuma sun zo ne bayan City ta ki biyan Wolves fam miliyan 60 din da ta nema kan Nunes.
City ta so ta karfafa bangaren wasan tsakiyarta tun kafin Kevin de Bruyne ya samu rauni a kafarsa wanda zai iya sa ya yi jinyar watanni hudu.
Dan wasan West Ham Lucas Paqueta ya kasance zabin farko kafin a bayyana cewa hukumar kwallon kafa ta Ingila na binciken dan wasan na kasar Brazil, mai shekara 25, kan yuwuwar keta ka'idojin yin caca.
Kocin Wolves Gary O'Neil ya ce bayan nasarar cin kofin Carabao da suka yi da Blackpool ranar Talata cewa yana tsammanin Nunes zai ci gaba da zama a kulob din bayan ranar Juma'a.











