Chelsea ta ci wasa biyu a jere a Premier karon farko tun bayan Maris

Premier League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Burnley ta yi rashin nasara a hannun Chelsea da ci 4-1 a wasan mako na takwas a gasar Premier League ranar Asabar a Turf Moor.

A minti na 15 Burnly ta fara cin kwallo ta hannun Wilson Odobert, ya zama na farko a ƙungiyar da ya ci kwallo mai shekara 18 a tarihi.

Daf da hutu ne Chelsea ta farke bayan da Burnley ta ci gida ta hannun Ameen Al-Dakhil, haka suka je hutu ana 1-1.

Minti biyar da komawa zagaye na biyu ne Cole Palmer ya ci wa Chelsea na biyu a bugun fenariti ya zama matashi na biyu da ya ci bugun daga kai sai mai tsaron raga a ƙungiyar.

Wanda yake riƙe da tarihin a Chelsea shi ne Oscar a karawa da Aston Villa a Disambar 2012 mai shekara 21 da kwana 105, shi kuwa Palmer yana da shekara 21 da kwana 154.

Raheem Sterling ne ya ci na uku ya zama na farko da ya zura kwallo a ragar Burnley a ƙungiya uku, wato a Liverpool da Manchester City da kuma Chelsea.

Ƙungiyar Stamford Bridge ta zura na huɗu ne a raga ta hannun Nicolas Jackson.

Haka kuma karo na 15 da ya zura kwallo a ragar ƙungiya sabuwar da ta koma buga Premier League a fafatawa 18 da ya fuskance su.

Karon farko da Chelsea ta ci wasan Premier biyu a jere tun bayan watan Maris.

Burnly ta zama ta biyar da ta yi rashin nasara biyar da fara kakar tamaula, bayan Manchester United a 1930/31 da Portsmouth a 2009/10.

Sauran sun haɗa da Bolton a 2011/12 da kuma Newcastle United a 2018/19 a irin wannan rashin ƙoƙarin.

Haka kuma ta zama ta farko da ta samu gurbin Premier, amma ta kasa cin wasa biyar a gida daga fara kakar nan, shi kansa koci, Vincent Kompany ya zama na farko da ya kasa cin wasa biyar a gida da fara wasannin bana.