Ko Hamas za ta iya ci gaba da jure wa yaƙin Gaza?

Mayaƙan Al-Qassam Brigades, bangaren soji na Hamas

Asalin hoton, EPA-EFE / REX / Shutterstock

Bayanan hoto, Mayaƙan Al-Qassam Brigades, bangaren soji na Hamas
    • Marubuci, Hanan Razek
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Correspondent, BBC News Arabic
    • Marubuci, Edited by Andrew Webb
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Global Journalism
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 8

Majalisar tsaron Isra'ila ta amince da shirin Firaiminista Benjamin Netanyahu na karɓe iko da Birnin Gaza. Tun farko ya nuna aniyarsa ta karɓe iko da ɗaukacin Zirin Gaza.

Yanzu mece ce makomar Hamas a Gaza kuma ya lamurra za su kasance gare ta?

Kwanaki ƙalilan gabanin kalamin Netanyahu, Hamas ta yi iƙirarin cewa ba za ta ajiye makamanta ba har sai an samar da ƙasar Falasɗinawa mai ƴanci. Ta faɗi hakan ne a amatsayin martani game da wata buƙata ta Amurka da Isra'ila cikin sharuɗɗan tsagaita wuta.

Isra'ila na ɗaukar ajiye makaman Hamas a matsayin ɗaya daga cikin muhimman sharuɗɗan da za a cika kafin cimma duk wata yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin.

A wani taron ƙasashen duniya na Majalisar Dinkin Duniya wanda Saudiyya da Faransa suka jagoranta a makon da ya gabata a birnin New York, ƙasashe 17 da Tarayyar Turai da kuma Ƙungiyar ƙasashen Larabawa sun miƙa wata buƙata.

Inda suka yi kira ga Hamas ta ajiye makamanta sannan ta sauka daga jagorancin Gaza domin kawo ƙarshen yakin.

Masar da Qatar waɗanda suke yawan shiga tsakani kan batun kawo zaman lafiya a Gaza sun sanya sunayensu a cikin takardar sanarwar. Sai dai Isra'ila da Amurka ba su sanya hannu kan takardar ba.

Dubban ɗaruruwa Falasɗinawa ne ke fama da yunwa a Gaza sanadiyyar toshe hanyoyin kai agaji zuwa yankin da Isra'ila ta yi

Asalin hoton, Mohammed Saber / EPA / Shutterstock

Bayanan hoto, Dubban ɗaruruwa Falasɗinawa ne ke fama da yunwa a Gaza sanadiyyar toshe hanyoyin kai agaji zuwa yankin da Isra'ila ta yi

Hamas za ta ci gaba da yaƙi

Ɗaya daga cikin shugabannin Hamas ya shaida wa kafar talabijin ta Al-Jazeera cewa ƙungiyar ba za ta taɓa miƙa wuya ba.

Bayanin da ya yi na nua cewa ƙungiyar na da aniyar ci gaba da yaƙi har sai an tabbatar da ƙasar Falasɗinawa mai ƴanci.

Ghazi Hamad, wanda ya yi magana da Al-Jazeera

Asalin hoton, Amr Alfiky / Reuters

Bayanan hoto, Ghazi Hamad, wanda ya yi magana da Al-Jazeera

Hossam Al-Dajany, wani farfesan harkokin siyasa a jami'ar Al'ummah University ta Gaza, ya yi amannar cewa bayan kammala taron da aka yi, yawancin kafafen yaɗa labarai sun mayar da hankali ne kan babi na 11 na yarjejeniyar New York.

Yarjejeniyar da aka fitar ta bayyana abin da ke ƙunshe a babi na 11, wanda ke cewa: "Wajibi ne gudanarwa da tabbatar da doka da tsaron ɗaukacin yankunan Falasɗinawa ya kasance a hannun Hukumar gudanarwar Falasɗinawa, wato Palestinian Authority.

Al-Dajany ya bayyana cewa wasu daga cikin sassa 41 na yarjejeniyar sun buƙaci a kafa ƙasar Falasɗinawa wadda za ta kasance daura da daura da Isra'ila. Ya ce hakan na nufin yarjejeniyar ta ambato matakai daban-daban na ƙirƙirar ƙasar Falasɗinawa.

Wata ma'aikaciyar kungiyar Red Cross a kusa da mayakan Hamas lokacin miƙa gawarwakin wasu ƴan Isra'ila da aka yi garkuwa da su a kudancin Zirin Gaza a watan Fabarairu

Asalin hoton, Haitham Imad / EPA-EFE / REX / Shutterstock

Bayanan hoto, Wata ma'aikaciyar kungiyar Red Cross a kusa da mayakan Hamas lokacin miƙa gawarwakin wasu ƴan Isra'ila da aka yi garkuwa da su a kudancin Zirin Gaza a watan Fabarairu

Ƙasar Falasɗinawa

Ƙasashen Amurka da Birtaniya da sauran ƙasashen yammacin duniya sun ayyana Hamas a matsayin ƙungiyar ta'addanci.

Ta bayyana cewa da zarar aka samar da ƙasar Falasɗinawa, za ta miƙa makamanta ga gwamnatin Falasɗinawa da za a kafa.

Wasu mayaƙan Hamas a lokacin miƙa mutanen da ake garkuwa da su a cikin watan Fabarairu

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wasu mayaƙan Hamas a lokacin miƙa mutanen da ake garkuwa da su a cikin watan Fabarairu

To sai dai masu lura da al'amuran yau da kullun sun ce ƙungiyar ta rasa ikon da take da shi a sassa da dama na Gaza.

Har yanzu Hamas ce ake gani a matsayin wadda ke mulkin Gaza.

A baya-baya nan ta ƙaddamar da wata rundunar tsaro da ake kira Sahm - wadda take aikin tabbatar da bin doka tsakanin al'umma domin hana wawason kayan agaji.

Falasdinawa fararen hula sun sha nuna fushi da ƙungiyar Hamas, sai dai mayaƙanta sun riƙa murƙushe masu zanga-zanga.

Abinci da sauran kayan tallafi sun yi ƙaranci, inda hukumomin agaji da kuma Majalisar Dinkin Duniya suka yi gargadin cewa mutane na mutuwa sanadiyyar yunwa.

Yaran Falasdinwa na cuncurundon karbar abincin agaji

Asalin hoton, Khamis Al-Rifi / Reuters

Masharhanta da dama sun yi imanin cewa abubuwa sun yi wa Hamas yawa kuma ba ta taɓa tunanin za a raunana ta haka ba a lokacin da ta ƙaddamar da hari kan Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba.

Mayaƙan Hamas na raguwa, wata 22 bayan martanin da Isra'ila ta fara kan harin da Hamas ta kai mata.

Mayaƙan Hamas na rundunar Izz ad-Din al-Qassam a Khan Yunis, kudancin Gazaranar 15  ga watan Fabarairun 2025.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Mayaƙan Hamas

Majiyoyin cikin Gaza na cewa har yanzu Hamas tana da makamai, sai dai makaman nata na ƙarewa.

Sun ce yanzu ƙungiyar ta mayar da hankali ne wajen sake sarrafa makaman da suka samu daga sojojin Isra'ila - musamman bama-baman da ba su fashe ba.

Mayaƙan na amfani da sinadaran da ke cikin bam ɗin wajen hada abubuwan fashewa da suke amfani da su wajen kai wa sojojin Isra'ila farmaki.

Wasu yara Falasdinawa na wasa a kusa da buraguzan gidajensu

Asalin hoton, Mohammed Saber / EPA-EFE / REX / Shutterstock

Bayanan hoto, Hare-haren Isra'ila sun lalata mafi yawa na yankin Gaza

Isra'ila ta hana ƴan jaridar BBC shiga Gaza, saboda haka ba za mu iya tantance gaskiyar hakan ba.

A yankin Gabas ta Tsakiya kuwa yanzu Hamas ba ta da sauran ƙawaye masu yawa. Bayan yaƙin kwana 12 da aka yi tsakanin Isra'ila da Iran, yanzu Iran ba ta da ƙarfin tallafa wa Hamas kamar yadda ta saba.

Ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon mai alaƙa da Iran, ita ma an raunana ta bayan da Isra'ila ta kashe shugabanninta.

Haka nan Hezbollah na fuskantar matsi daga gwamnatin Lebanon na ta ajiye makamanta, saboda haka ba ta da ƙarfin kai ɗauki a wata ƙasa.

Sakataren harkokin waje na Birtaniya David Lammy (centre left) ya rungumi Firaiministan Falasɗinawa Mohammad Mustafa a ginin Majalisar Dinkin Duniya ranar 29 ga watan Yuli 2025.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Sakataren harkokin waje na Birtaniya David Lammy (centre left) ya rungumi Firaiministan Falasɗinawa Mohammad Mustafa a ginin Majalisar Dinkin Duniya ranar 29 ga watan Yuli 2025.

Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa

Ƙungiyar ƙasashen Larabawa ta sanya hannu kan yarjejeniyar New York wadda ta buƙaci Hamas ta jefar da makamanta.

Ƙungiyar na da ƙasashe 22, cikinsu har da waɗanda ke nuna sassauci kan Hamas, kamar Qatar.

Farfesa Yossi Mekelberg na cibiyar tattaunawa kan lamurran duniya ta Cahtham House da ke Landan na ganin cewa Isra'ila da Amurka na nan kan matsayinsu.

Amma ya ce ƙasashen Larabawa sun sauya matsayarsu. Ya ce wata ƙila matsi daga ƙasashen Larabawa da sauran masu ruwa da tsaki a yankin zai sa Hamas ta zama "saniyar ware".

Ana yiwa gawarwakin wasu Falasdinwa da Isra'ila ta hallaka su hudu sallah

Asalin hoton, Dawoud Abu Alkas / Reuters

Bayanan hoto, Ma'aikatar lafiya ta Hamas da ke Gaza ta ce hare-haren Isra'ila sun kashe sama da mutum 60,000

Mutanen da ake garkuwa da su

Babban abin da Hamas ta riƙe a matsayin makamanita a duk wata tattaunawa shi ne mutanen da take garkuwa da su.

Ƙungiyar ta yi garkuwa da mutum 251 a lokacin da ta kai gagarumin hari kan Isra'ila, inda ta kashe kimanin mutum 1,200.

Hukumar lafiya ta Hamas a Gaza ta ce hare-haren Isra'ila sun kashe sama da mutum 60,000 a yakin da ake ci gaba da gwabzawa.

Amurka ta ce ta yi imanin cewa akwai sauran aƙalla mutane 20 masu rai cikin waɗanda ake garkuwa da su, bayan wasu daga cikinsu sun mutu, wasu kuma an mayar da su ga Isra'ila.

Hamas ta saki bidiyon mutumin da take garkuwa da shi Evatar David a farkon watan Agusta, inda aka gan shi a tamuƙe ya sha wahala.

Masu sharhi na ganin cewa Hamas na sa ran bidiyon zai sanya iyalan waɗanda ake garkuwa da su su matsa wa Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu lamba wajen kawo ƙarshen yaƙin.

Bayan sakin bidiyon, iyalan sun yi kira ga Netanyhau da ya fifita batun ceto waɗanda ake garkuwa da su.

Shugabannin Hamas da aka kashe daga ranar 7 ga watan Oktoba 2023

Jerin shugabannin Hamas da Isra'ila ta kashe tun ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

Tun daga Oktoban 2023, Isra’ila ta kashe shugabannin Hamas da dama, cikinhar da babban shugabansu Ismail Haniyeh. An kashe a wani hari a babban birnin Iran.

Haka nan kuma Isra’ila ta kashe Yahya Sinwar, wanda shi ne ake zargi da kitsa hare-haren ranar 7 ga watan Oktoba.

Meckleberg ya ce ra’ayin shugabannin Hamas da ke cikin Gaza ya sha bamban da shugabanninta da ke waje.

To amma a cewarsa idan har kungiyar na so ta ci gaba da wanzuwa to wajibi ne shugabanninta su dauki matakai masu tsauri.

Kuma bayan matakin Netanyahu na ranar Alhamis 7 ga watan Agustan 2025 na aniyar “karbe iko” da Gaza da kuma “kawar da Hamas”, damarmakin da Hamas ke da su na ci gaba da tsukewa a kullu-yaumin.

Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sanar da aniyar karbe iko da Birnin Gaza

Makomar Hamas

To, ko Hamas za ta iya kaiwa har karshen yakin Gaza?

Idan aka samar da kasar Falasdinawa, kuma Hamas ta cika alkawarinta, za ta jefar da makamanta ke nan.

To sai dai batun samar da kasar Falasdinawa da alama akwai sauran aiki kafin a yi hakan, sai dai idan gwamnatin Isra’ila ta sauya matsayarta.

Ko da hakan ta faru, hakan ba yana nufin cewa Hamas ta mutu ba ke nan baki daya.

Yossie Mekelberg na cibiyar nazari kan lamurran duniya ta Chatham House ya yi hasashen cewa kungiyar za ta iya sake samun damar farfadowarta ta wata sigar a nan gaba kuma ta ci gaba da taka rawa a fagen siyasar Falasdinawa.

Wannan zai iya faruwa a ciki ko wajen yankunan Falasdinawa.

Sai dai duk wadannan abubuwa sun dogara ne ga matsayar Isra’ila game da batun kafa kasar Falasdinawa da kuma sauran goyon bayan da zai rage wa Hamas bayan wannan mummunan hali da Gaza ke ciki.

Gine-ginen da Isra'ila ta lalata a arewacin Gaza

Asalin hoton, Amir Cohen / Reuters

Bayanan hoto, Gine-ginen da Isra'ila ta lalata a arewacin Gaza