Ƙungiyoyin Saudiyya na zawarcin Salah, Lyon za ta ɗauki aron Endrick

Asalin hoton, Getty Images
Roma na zawarcin ɗan wasan Netherlands mai shekara 24, Joshua Zirkzee, daga Manchester United. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Crystal Palace za ta shiga cinikin ɗan wasan bayan Manchester City da Netherlands mai shekara 30, a kaka mai zuwa. (Teamtalk)
Ƙungiyoyin gasar Saudi Pro ta Saudiyya na ci gaba da rubibin ɗan wasan gaban Masar da Liverpool, Mohamed Salah, mai shekara 33. (TBR Football)
Tottenham za ta shiga zawarcin ɗan wasan gaban Ingila da West Ham mai shekara 28, Jarrod Bowen. (Fichajes - in Spanish)
Fabio Carvalho ya shirya tataunawa da Brentford a kan makomarsa, kuma ɗan wasan tsakiyar Portugal ɗin mai shekara 23 na son cinikin ya tabbata a watan Janairu.(Sky Sports)
Chelsea are planning to replace manager Enzo Maresca with Bournemouth boss Andoni Iraola. (Caught Offside)
Lyon na tattaunawa da ɗan wasan gaban Brazil mai shekara 19, Endrick, domin taka mata leda na wata shida a matsayin aro daga Real Madrid a watan Janairu. (Mail)
Ɗan wasan gaban Brazil Neymar ya shirya sabinta sharuɗɗan kwangilarsa da Santos bayan ɗan wasan mai shekara 33 ya shirya komawa taka leda a Turai kafin gasar cin kofin duniya a baɗi.(AS - in Spanish)
Celtic na neman kocin Club Brugge, Nicky Hayen a matsayin wanda zai maye gurbin Brendan Rodgers. (Nieuwsblad - in Dutch)
Tsohon kocin Italiya da Napoli, Luciano Spalletti ya amince ya zama kocin Juventus har zuwa watan Yunin 2026, tare da zaɓin tsawaita kwangilar nan gaba. (Sky Italia - in Italian)












