Paqueta zai bar West Ham, Tottenham na zawarcin Marc-Andre ter Stegen

Marc-Andre ter Stegen

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Ɗan wasan tsakiyar Brazil mai shekara 28, Lucas Paqueta, na shirin barin West Ham a watan Janairu. (Times - subscription required)

Tottenham na fatan ɗauko ɗan wasan tsakiyar Scotland mai shekara 28, Scott McTominay daga Napoli. (Teamtalk)

Napoli za ta ƙara yunƙurin sayen ɗan wasan tsakiyar Ingila mai shekara 20, Kobbie Mainoo daga Manchester United a watan Janairu. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Manchester City ta fara tattaunawa da ɗan wasan tsakiyar Sifaniya mai shekara 29, Rodri, a kan ƙulla sabuwar kwangila da shi kafin ƙarshen shekarar nan(TBR Football)

Tottenham za ta ɗauko Marc-Andre ter Stegen daga Barcelona a watan Janairu, amma mai tsaron gidan na Jamus mai shekara 33 na da zaɓin tafiya aro a Chelsea. (Teamtalk)

Chelsea da Tottenham sun nuna sha'awar ɗan wasan tsakiyar Ingila mai shekara 23, Morgan Rogers, amma Aston Villa ta fara tattauna ƙulla sabuwar kwangila da ɗan wasan.(Fabrizio Romano)

Fabio Carvalho zai bar Brentford a watan Janairu, amma ana duba yadda ƙungiyar za ta iya sayen ɗan wasan na Portugal mai shekara 23.

Liverpool na cikin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan bayan Club Brugge, mai shekara 21, Joel Ordonez. (Ekrem Konur)

Manchester United na zawarcin ɗan wasan gaban AIK da Sweden mai shekara 16, Kevin Filling. (Florian Plettenberg)