Yadda ɓarnar da Rasha ta yi a Ukraine ta jefa ƙasar cikin duhu

Birnin Kyiv

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

 

'Yan kasar Ukraine na shirin fuskantar hunturu biyu zuwa uku ba tare da wutar lantarki ba sakamakon katsewar wutar da hare-haren Rasha suka haifar, a cewar matar shugaban ƙasar, Olena Zelenska.

A faɗin Ukaine, hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuka sun jefa miliyoyin ‘yan kasar cikin rashin makamashin amfani da dumama gida da ruwa.

Yaya girman ɓarnar da Rasha ta yi wa fannin makamashin Ukraine?

Bayan fuskantar koma-baya a filin daga, dakarun Rasha sun ba da karfi wajen kai hare-hare a cibiyoyin samar da lantarki, defon adana fetur da ayyukan samar da ruwa.

Kamfanin lantarkin Ukraine, Ukrenergo, ya ce asarar da aka yi wa cibiyoyin lantarki ta kai matakin da ba za su iya samar da kusan kashi 50 cikin 100 na bukatar makamashi a kasar ba.

Shugaba Volodymyr Zelensky ya ce ‘yan kasar kusan miliyan shida ke cikin duhu saboda rashin makamashi.

Ya ce hare-haren sun katse samar da wuta daga Kyiv zuwa Odesa da ke kudancin kasar, da kuma Vinntysia da ke yammaci.

Ya ce wannan yanayi da ake ciki na nufin mutane da dama na cikin yanayi mai muni, ba sa iya dumama gidansu yayin da sanyi ya kai yanayi mai tsanani a sassan Ukraine.

Wani kamfanin lantarki, Yasno, ya ce 'yan Ukraine na iya zama cikin rashin wuta har zuwa watan Maris.

Kungiyar Tarayyar Turai ta ba da kuɗi domin a sayi kayayyakin samar da wuta irin su janareto da keburan wuta domin dawo da wutar, da tallafin asusun inganta lantarki na Ukraine.

Ya ɓarnar take shafar cibiyoyin makamashin nukiliyar Ukraine?

An kashe cibiyoyi uku na makamashin nukilliya na tsawon kwanaki biyu saboda hare-haren sama.

Kwararru a Majalisar Dinkun Duniya sun nuna damuwa kan hare-haren da ake kai wa a yankunan cibiyar makamashi ta Zaporizhzhia – mafi girma a Turai – da suke ganin na iya jawo fitar turirin nukiliya mai hadari.

Makamai sun fada a kusa da injin da ke sarrafa nukiliyar da lalata wani yanki da ake adana wasu kayayyakin da aka tace daga cibiyar, sai dai hakan bai haddasa gagarumar ɓarna ba.

Ukraine da Rasha sun zargi junansu da kai wadannan hare-hare.

Me ya sa Rasha ke harar cibiyoyin wutar lantarki?

Al'ummar Kherson

Asalin hoton, Getty Images

Hare-hare kan cibiyoyin lantarki wani kokari ne na daƙile kwarin-gwiwar al’ummar Ukraine fararen-hula, a cewar Marina Miron, wata kwararriyar mai bincike kan tsaro a Kwalajen Kings ta Landan.

"Russia na ganin idan mutane suka soma gajiya da matsi, za su iya yi wa gwamnati bore," a cewarta.

Sai dai Olena Zelenska, ta faɗa wa BBC cewa a shirye 'yan Ukraine suke su tunkari kowanne irin yanayi ba tare da lantarki ba, indai hakan zai tabbatar musu da cikakken ‘yanci da kuma burinsu na shiga kungiyar Tarayyar Turai.

Gwamnatin Ukraine ta bukaci fararen-hula su fice daga wasu yankuna da ake da wasu muhimman abubuwa kamar tashoshin lantarki, da hare-hare ya yi muni, maimakon kokari zama a wannan yanayi cikin huturu.

Yana shawararta mutane mazauna Kherson da Mykolaiv, da ke kudu maso yammacin Ukraine, su koma yankunan yammaci ko tsakiyar kasar da zama.

Yaya girman ɓarnar hare-haren Rasha a fannin lafiya?

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce bayananta sun nuna cewa an kai hare-hare 703, da barazanar hari ga gine-ginen kiwon lafiya a Ukraine tun lokacin da Rasha ta soma mamaya a kasar a watan Fabarairu.

Daruruwan asibitoci da gine-ginen kula da lafiya yanzu haka "ba sa aiki, akwai karancin fetur da ruwa da lantarki domin biyan bukatun yau da kullum," a cewar Dakta Hans Kluge, daraktan WHO a Turai. Ya ce wannan yanayi na jefa rayuwar miliyoyin mutane cikin haɗari.

WHO ta bukaci a tsagaita wuta a wasu yankunan domin bayar da damar shigar da agajin kiwon lafiya ga yankunan da Rasha ta mamaye na Donbas, da kuma sabbin yankunan da Ukraine suka sake kwatowa, irin su 'yankin Kherson.

Shin hare-hare kan cibiyoyin lantarki da kiwon lafiya laifukan yaƙi ne?

Karkashin yarjejeniyar da aka cimma a Geneva, kai hari da gangan kan fararen-hula, ko kuma gine-ginensu masu muhimmanci da zai iya shafar rayuwarsu, ana iya bayyana shi da aikata laifukan yaƙi.

Dr Kluge ya bayyana hare-hare kan cibiyoyin lafiya da "saba dokokin jin-kai na kasa da kasa da kuma dokokin yaki".

Shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen ta ce hare-haren Rasha na makami mai linzami da jirage marasa matuka kan cibiyoyin lantarki da sauran cibiyoyin samar da makamashi a Ukraine "ba su da maraba da ta'addanci".

Ta ce "kai hari kai-tsaye kan gine-ginen amfanin fararen-hula" laifukan yaki ne.