'Yan Ukraine miliyan 10 na cikin duhu sakamakon hare-haren Rasha

Shugaba Zelensky ya ce 'yan Ukraine miliyan 10 ba su da wutar lantarki bayan da Rasha ta sake kai musu hare-haren makamai masu linzami.
Akalla mutum bakwai sun rasa rayukansu a hare-haren inda ake fargabar adadin zai iya karuwa.
A jawabin da yake yi kowa ne dare Shugaba Zelensky ya ce gwamnatinsa tana duk wani abin da ya kamata domin mayar da wutar lantarkin.
" Muna duk wani abin da ya kamata domin dawo da wutar lantarkin ," In ji Mista Zelensky a jawabinsa na dare .
Sai dai ya ce na'urar kare sararin samaniyar Ukraine ta harbo makamai masu linzami guda shida da jiragem sama marassa matuka biyar
A ranar Alhamis ne Rasha ta sake yi wa Ukraine din luguden wuta abin da kuma ya shafi fannin wutar lantarkin kasar da wasu gine- ginen farar hula a kwanaki kasa da biyu bayan daya daga cikin hare-haren bama-bamai mafiya muni.
Mutum bakwai sun rasa rayukansu lokacin da wani makami mai linzami ya fada a gidansu a garin Vilnyansk kusa da garin Zaporizhzhia a cewar fadar shugaban kasa.
Jami'an Ukraine sun ce wata cibiyar samar da iskar gas da kuma makamai a garin Dnipro na cikin wuraren da aka kai wa hari.
Wuraren da matsalar rashin wutar lantarkin ta shafa sun hada da birnin Kyiv da Vimmystia da Odesa da kuma Sumy.
Shugaba Zelenky ya zargi Rasha da lalata makamashin da kasar take amfani da shi wajen samun wutar lantarki tare kuma da dumama daki.











