Ƙasa mai yawan musulmai wadda aka haramta wa yara mata sanya hijabi a sakandare

Yarinya sanye da hijabi
An wallafa

Kazakhstan ta kasance ɗaya daga cikin kasashen da musulmai ke da rinjaye a cikin al'umarta wadda kuma ta sanya haramcin sanya hijabi ga dalibai mata.

A shekarar 2016 ne aka fara sanya haramcin, sai dai har yanzu ana cece-kuce a kan batun, inda iyaye musulmai ke kare damar da kundin tsarin mulkin ƙasar ta bai wa ƴaƴansu na ƴancin samun ilimi.

Anelya mai shekara 13 a duniya tana matakin karatu na bakwai a Karanganda, kuma burinta ya cika na samun gurbi a makaranta ta-gani-ta faɗa ta Nazarbayev Intellectual School (NIS).

Sunan tsohon shugaban ƙasar na Kazakhstan, Nursultan Nazarbayev aka sanya wa makarantar. Kuma burin Anelya shi ne ta bi sawunsa don zama mace ta farko da za ta rike muƙamin shugabancin ƙasar.

Anelya yarinya ce siririya kuma doguwa wadda ta yi nasara a gasar da aka shirya a matakin yanki da kuma ƙasa baki ɗaya. Ta kuma samu sakamako mai kyau da ya sanya ta zama ta 16 a cikin kusan ɗalibai 800 da suka zana jarrabawar neman gurbi a makarantar.

A watan Agusta ta fara halartar azuzuwan share fage, sai dai a ranar farko aka yi wa iyayenta waya cewa su zo makarantar ana neman su - inda aka fada musu cewa ƴarsu ba za ta iya karatu a makarantar ba.

Dalili kuwa shi ne ɗankwalinta, wanda ta fara ɗaurawa a lokacin da ta shiga shekara 13, kamar yadda musulunci ya buƙaci ƴanmata su fara rufe kansu a lokacin da suka balaga.

"Lokacin da na ɗaura ɗankwalina na je NIS, ban ji na zama wata dabam ba da sauran ɗalibai- sutura ce kawai, ba ta da wani tasiri a kan karatuna ko dangantakata da sauran ɗalibai, abokan karatuna ma bai dame su ba. In ji Anelya.

Littafi mai zane
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Al'ummar Kazakhstan mafiya yawansu musulmai ne - a ƙidayar da aka yi a ƙasar a shekarar 2022 ya nuna cewa kashi 69 cikin ɗari na mutanen ƙasar Musulmai ne. Sai dai wasu nazarce-nazarcen da aka yi sun nuna cewa kashi ɗaya bisa uku ne kawai suke ɗaukar kansu a matsayin masu yin addinin sau-da-ƙafa.

Shugaban ƙasar Kassym-Jomart Tokayev ya fito fili ya bayyana cewa ya na bin addinin Islama. Ya je aikin hajji a shekarar 2022 kuma ya gayyaci jami'an gwamnati da manyan mutane gidansa domin yin buɗabaki a gidansa a bara. Sai dai a hukumance Kazakhstan ƙasa ce da babu ruwanta da addini a tsarin gudanarwarta.

Gwamman ɗalibai kamar Anelya sun fuskanci irin wannan matsalar a Karaganda, wani birni mai masana'antu da mafiya yawan alummarta ke magana da harshen Rasha. A watan Oktoba, wasu rahotanni sun ce iyayen yara mata 47 na fuskantar shari'a kan gazawa su ɗauki nauyin da ya rataya a kansu "kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadi dokar da ta shafi ilimi a ƙasar ta Kazakhstan".

A shekarar 2016 ne ma'aikatar ilimi ta ƙasar ta fitar da wata doka wadda ta ce daga sannan sanya duk wani tufafi da ke nuni da wani addidini a matsayin kayan makarantar ya haramta a makarantu".

Zane da ke nuna malama da wasu ɗalibai kansu a rufe da hijabi

Ga wasu iyaye da kuma masu rajin kare haƙƙi abu ne da bai kamata a lamunce shi ba makarantu su dinga nuna fifiko ga wani umarni na ma'aikata a kan kundin tsarin mulkin ƙasar wanda ya bai wa kowane ɗan ƙasa ƴancin samun ilimi kyauta a cibiyoyin ilimi na gwamnati.

Anelya ya nemi ƙarin haske daga ofishin mai gabatar da ƙara na gwamnati da kuma ma'aikatar ilimi -amma haƙarsa ba ta cimma ruwa ba.

An ɗauki shekaru tun lokacin da aka fara samun iyayen da suka fuskanci hukunci saboda ƴaƴansu da suka ɗaura ɗankwali, kuma lamarin ya shafi faɗin ƙasar. A shekarar 2018, yankin Aktobe, an ci tarar wasu iyaye saboda "ƙin yin kayan makaranta kamar yadda aka buƙata, " haka a yankin Akmola, an kafa wata hukumar domin magance irin waɗannan batutuwa a wannan shekarar.

"An samu lokutan da aka tilasta wa wasu yara cire ɗankwalinsu saboda matsin lamba daga hukumomin makarantu," a cewar wani mai rajin kare haƙƙin ɗan’adam, Zhasulan Aitmagambetov, wanda ke taimaka wa iyalan da ke aiki da iyalai masu bin addini a irin waɗannan yanayi. " kaɗan da suka ƙi amincewa su cire hijabin sun daina zuwa makaranta. Matsin lambar na rage yawan masu bin addini a makarantu."

Gwamnatin Kazakhstan ta jaddada tsarin tafiyar da harkokin ƙasar ba tare da sanya addini ba - wanda shi ma kundin tsarin mulki ne ya amince da hakan - Idan aka zo batun sanya ɗankwali a makaranta.

"Ya kamata ko da yaushe mu san cewa da farkon fari makaranta cibiya ce ta ilimi inda ake zuwa domin samun ilimi," a cewar shugabaTokayev a watan Oktoba. "Kuma na yi amanna cewa zai fi dacewa idan muka bar yara su yi zaɓin abin da suke so bayan sun girma bayan sun san mece ce duniya."

"Babu wani abun da ke ɓoye da kuma kwakkwarar ma'anar "bin tsarin da ba ruwan shi da addini ga ƙasa," daga hukumomi ko kuma kwararru," a cewar Asyltay Tasbolat, wani manazarcin ilimin addinai kuma mai bincike a cibiyar falsafal kimiyyar siyasa da nazarin addinai ta Almaty.

"Al'ummarmu har yanzu wayewarsu ba ta kai ba, don kowane bangaren da ke cikin muhawarar na fassara "tsarin ba ruwan mu da addini" a yadda ya fahimce shi. Wasu na ɗaukarsa a matsayin rashin imani da Allah."

Zanen mata masu hijabi

Ƙasashe da dama sun sanya dokokin da ke hana sanya wani nau'in kaya na musulmi mata a wuraren na al'umma. Inda ya fi shafar abun da ake rufe kai ha shi kamar mayafi da niƙab, ba hijab ba. Abu ne da ba a saba gani ba ga ƙasar da ta fi yawan musulmai ta sanya irin wannan haramcin, irin waɗanannan ƙasashen sun haɗa da makwabtan Kazakhstan, wato Uzbekistan da kuma Tajikistan.

Barin addini a ƙarkashin ikon ƙasa abu ne da Kazakhstan ta dade tana yi tun lokacin haɗaɗɗiyar daular Soviet, USSR. A wancan lokaci ƙasashen biyar na tsakiyar Asiya na ƙarƙashin kulawar wata hukumar gudanarwa ta (Sadum), wadda aka kafa a 1943, kuma aka tsarata kan manufar dakushe ƙungiyoyin addinai.

Bayan samun ƴancin kai hukumomin Kazakh ta dakatar da muzgunawa mabiya addinai. ƙungiyoyin addini suka bunƙasa, aka fara gina masallatai -daga kaɗan da ake da su a lokacin daular Soviet, a yanzu sun kusa 3000.

Amma an maye gurbin Sadum da DUMK - hukumar addinin musulunci ta Kazakhstan - wadda aka ɗorawa alhakin bunƙasa addinin musulci na ainihi wanda ya zo daidai da al'adun ƙasar da kuma tanade-tanade na tsarin da ba ruwansa da addini.

Zanen wata malama da wasu ɗalibai masu hijabi

Ga gwamnatin Kazakhtan barin addini a ƙarƙashin ikonta batu ne da ya shafi tsaron ƙasa. Masu bincike sun ce tun shekarar 2005, tasirin ƙungiyoyin masu iƙirarin Islama na arewaci, a yankin Afghanistan-Pakistan da Syria da Iraqi tashe-tashen hankula masu nasaba da addini da masu tsattsauran ra'ayi ke haddasawa na ƙaruwa a ƙasar ta Kazakhtan.

A shekarar 2011, Kazakhstan ta fuskanci harin ƙunar baƙin wake na farko, kuma a shekarar 2016 aka kashe mutane 25 a wani hari kan wasu shagunan makamai da sansanin soji. Shugaban ƙasar na wancan lokaci Nursultan Nazarbayev, ya bayyana waɗanda suka kai harin da cewa reshen ƙungiyar Islama ce ta Salafi.

A shekaraun da suka biyo baya gwamnati ta sanya takunkumai a kan harkokin addini da suka haɗa da tilastawa ƙungiyoyin addini na unguwanni su yi rajisata da gwamnati da kuma haramta dukkanin abubuwan addini a gidaje.

Sai dai a yayin da gwamnati take kare matakan da ta ɗauka da cewa tana kare ƙasar ne daga "tsauraran aƙodu, " masu kare haƙƙin bil'adama na cewa dokokin suna take haƙƙin mabiya addini - tare da bai wa ƙasa ƙarfin ikon a kan ƙungoyoyin addini.

A watan Oktoba, gwamnati ta sanar da aniyarta na yin dokar ta'addanaci da tsattauran addini. A cewar Aida Balayeva, ministar al'adu da yaɗa labarai, dokar za ta haramta sanya niƙab da sauran abubuwan rufe fuska a wuraren al'umma domin gane mutane. Sai dai ta ce ba babu niyyar hana sanya ɗankwalaye.

zanen wata yarinya zaune a ƙofar makaranta

Ga Anelya, bayan ta fuskanci takura saboda sanya ɗankwali zuwa makaranta daga baya an kore ta. Mahaifinta, Bolat Musin ya yi imanin cewa korar ta saɓawa doka: Ya shigar da ƙara yana neman a soke dokar makarantar da ta haramta sanya ɗankwali a matsayin wata alama ta addini da mayar da ƴarsa da kuma biyansu diyya.

"Hukumomin sai yawo da hanklinmu suke yi, daga nan su ce mu je can, ko kuma su ce kawai ta daina sa ɗankwalin mana. In ji shi. "muna neman kwakkwaran amsa daga gwamnati ta bamu haske kan abubuwan da za mu yi a matsayinmu na mabiya addini, me ya kamata mu yi, bai dace su bar mu da cewa zabin kawai shi ne mu bar addininmu ba idan muna so mu ci gaba da zama a cikin al'umma."

Hukumar makarantar NIS da ke Karaganda ta ƙi cewa uffan kan korar Anelya. Haka kuma ya zuwa lokacin da aka haɗa wannan rahoton ma'aikatar ilimi ta ƙasa ba ta ce komai ba game da buƙatar jin ta bakinta ba BBC ta yi.

Hukumar DUMK ta yi magana da taka-tsantsa, ba ta fito gaba-gadi ta soki gwamnati ba kan sanya haramcin, sai dai ta ce shari'ar musulunci ta buƙaci ƴanmata su sanya hijabi da zarar sun balaga. Hukumar na mai fatan gwamnatin za ta yi aiki da ra'ayinsu.

Mai rajin kare haƙkin ɗanAdam, Zhaslan Aitmagambetov ya ce mabiya addini ba su da wani zabi kuma na ilmantar da ƴaƴansu. A wasu sassan ƙasar ana samun makarantu masu zaman kansu, amma suna da tsada inda kuɗinsu ya kai 700,000 kuɗin kasar (tenge) a shekara - fiye da dalar Amurka 1,500. kasar tana kuma da wasu cibiyoyin koyar da addinin musulunci guda tara, sai dai ba dukkansu ne ke karɓar mata ba.

Bayan korarta daga makaratar ta NIS, mahaifin Anelya ya samar mata wani mai koyar da ita da harshen mutanen Rasha ta intanet. Amma idan ta yanke shawarar daina sanya ɗankwali don ta koma makaranta, babanta ya ce za su goya mata baya.

“Mutane da dama da na sani na cewa: ki cire ɗankwalin me ye a ciki? ki koma makaranta, Inji Anelya. "Amma ban taɓata tunanin yin hakn ba domin ɗankwalin ya zame mini jiki.”