Man City na tsaka mai mai wuya - Guardiola

Pep Guradiola

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kociyan Manchester City, Pep Guardiola ya ce suna tsaka mai wuya, bayan da 'yan wasan ƙungiyar da dama suke jinya.

'Yan wasa shida ne daga City da suka yi zaman benci masu lafiya a karawar da kungiyar ta ci Red Star Belgrade 3-1 a Champions League ranar Talata.

Wasa na bakwai da ta yi nasara a bana a jere kenan a dukkan fafatawar da ta yi, sai dai Bernardo Silva ya ji rauni a wasan na ranar Talata.

Dan kwallon Portugal ya bi sahun waɗanda ke jinya a ƙungiyar da suka haɗa da Kevin de Bruyne da Jack Grealish da Mateo Kovacic da kuma John Stones.

Hakan ya biyo bayan da City ta sayar da Riyad Mahrez da Cole Palmer da Aymeric Laporte da Ilkay Gundogan da ya koma Barcelona.

Haka shi ma Joao Cancelo ya bar Etihad da wasu matasan ƙungiyar da suka haɗa da Tommy Doyle da James McAtee da aka bayar da aronsu.

Kawo yanzu City za ta fuskanci wasan Premier League uku har da wanda za ta kara da Arsenal ranar 8 ga watan Oktoba da Carabao Cup da Newcastle.

Haka kuma City za ta je gidan RB Leipzig a Champions League daga nan a yi hutun zuwa buga wasannin kasa da kasa.

City ta kashe sama da fam miliyan 200 kan fara kakar nan, wajen sayen 'yan kwallo ciki har da Matheus Nunes, kan fam miliyan 53.