Issoufou na da hannu a cire Bazoum daga mulki – Tsohon jakadan Faransa

..

Asalin hoton, getty images

An wallafa

Tsohon jakadan Faransa a Nijar, Sylvain Itte ya shaida wa majalisar dokokin Faransa cewa tsohon shugaban Nijar Mohammadou Issoufou na da hannu kai tsaye wajen hamɓarar da gwamnatin shugaba Mohammed Bazoum.

A cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar, Itte ya yi zargin cewa shugaba Issoufou kodai ya kitsa juyin mulkin ko kuma ya goyi bayan hambarar da shugaba Bazoum, zargin da wani makusancin tsohon shugaban ƙasar ya musanta.

Tsohon jakadan na Faransa a Jamhuriyar Nijar, Sylvain Itté ya yi wata ganawa ne ta sirri da ‘yan kwamitin da ke kula da harkokin tsaron kasar da kuma dakarunta a majalisar dokokin Faransa a Paris domin ba su bahasi kan abin da ya kai ga juyin mulkin da sojoji suka yi a a Nijar a shekarar da ta gabata.

A bayannin da tsohon jakadan ya yi wa ‘yan majalisar ya yi ikirarin cewa tsohon shugaban Nijar Mohammadou Issoufou, ya goyi bayan hambarar da mutumin da ya gaje shi Mohammed Bazoum saboda wani sabani da suka samu a tsakaninsu da ke da alaƙa da kuɗin mai na ƙasar.

Tsohon jakadan ya ce, Bazoum ya nuna turjiya wajen yarda ya nada dan Mohammadou Issoufou a matsayin shugaban sabon kamfanin mai na kasar a wanna lokaci da gwamnati ke sa ran samun bunkasa a yawan man da take samarwa.

Tun a watan Nuwamba na shekarar da ta wuce ne Itte ya gabatar da wannan jawanbi ga ‘yan kwamitin tsaron na majalisar dokokin ta Faransa amma sai a kwanan nan ne majalisar dokokin ta wallafa shi.

Sai dai BBC ba ta samu jin ta bakin tsohon shugaba Issoufou na NIjar din kan wannan zargi ba, amma wani na hannun damansa, Assoumana Mohammadou ya musanta.

Ya ce tsohon shugaban ba shi da wani hannu a juyin mulkin, hasali dan shugaba Issoufou ma yana a tsare, "wanda hakan ke nuna cewa tsohon shugaban bai hada kai da sojojin wajen juyin mlkin ba."

"Wannan jakada kowa ya san yadda ya bar Nijar, a hautsine a cikin wulaƙanci," In ji Assoumana Mohammadou.

.

Asalin hoton, OTHER

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wasu kwanaki bayan juyin mulkin Shugaba Issoufou ya ɓara, inda a wasu sakonni a shafukan sada zumunta da muhawara ya ce ya kasance cikin wata tattaunawa ta shiga tsakani, domin mayar da Bazoum kan mulki.

Wani babban jigo a hambararriyar gwamnatin ya gaya wa BBC cewa an samu baraka a jamiyyar PNDS Tarayya mai mulkin cewa Issoufou, na jin haushi kan yadda Bazoum ba ya son daukar shawararsa wajen gudanar da mulkin kasar ta Nijar.

"A lokacin da shugaba Issoufou ya bar mulki idan har ya so da ya yi tazarce, babu wanda ya isa ya hana masa, saboda haka wadannan zantuntuka ne na mutanen da suka gaza, sai dai mu a wajen mu yanzu muke fahimtar inda aka dosa."

"Issoufou da magoya bayan PNDS sun kama ma Bazoum ɗari bisa ɗari, babu wata rashin jituwa tsakanin su," cewar Assoumana Mohammadou.

Tun bayan da ya hau mulki a 2021, Bazoum, ya kara karfafa hadin kai da alaka da Faransa da Amurka.

Ya rage karfin ikon kwamandojin sojin Nijar ya kuma kaddamar da shirye-shiryen yaki da cin hanci da rashawa, har wasu daga cikin mukarraban gwamnatin Issoufou, musamman a bangaren mai, wanda a dalilin hakan yake samun sabani da su.

Juyin mulkin da sojojin suka yi a watan Yuli na shekarar da ta gabata, wanda da dama aka yi Allah wadarai da shi daga wajen kasar, ya sa kungiyar kasashen Afirka ta Yamma Ecowas sanya wa Nijar din takunkumi.

Tun bayan juyin mulkin, sojojin karkashin ikon Janar Abdourahmane Tchiani sun yi wa hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum daurin talala a gidansa da ke fadar gwamnati a Yamai, kuma sun lashi takobin cewa ba za su sake shi ba.