Abu hudu da Blinken ya tattauna da Tinubu

..

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto, Anthony Blinken tare da Shugaban Najeriya Bola Tinubu
An wallafa

A ranar Laraba ne Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ke kammala wata ziyarar aiki da ya kai Najeriya a wani bangare na rangadin da yake a kasashen Nahiyar Afirka hudu.

Wannan dai na zuwa ne bayan ganawar da ya yi da Shugaban Najeriya Bola Tinubu da kuma wasu manyan jami'an gwamnatinsa a fadar Aso Rock da ke Abuja.

Blinken dai ya soma rangadin zuwa kasashen na Afirka a ranar 21 ga watan Janairu inda kuma zai kammala ranar 26. Ya fara zuwa Cape Verde sannan ya kai ziyara Ivory Coast, daga nan kuma ya wuce Najeriya. Kasa ta gaba kuma ta karshe a rangadin ita ce Angola.

Makasudin ziyarar zuwa kasashen shi ne tattauna kawancen kasuwanci tsakanin Amurka da Afirka da sauyin yanayi da lafiya da tsaro da sauran batutuwa.

Kalubalen tsaro a yammacin Afirka da kifar da gwamnati a Nijar a shekarar da ta gabata da kuma karuwar tasirin Rasha a yankin na daga cikin manyan batutuwan da rangadin na Blinken zai fi mayar da hankali a kan su.

Ministan harkokin wajen Najeriya Ambasada Yusuf Maitama Tuggar da takwaransa na yada labarai, Muhammad Idris sun yi wa BBC karin bayani game da abubuwan da tattaunawar ta Blinken da Tinubu ta mayar da hankali a kai.

Halin da ake ciki a yakin da Isra'ila take yi a Gaza

Ministan yada labarai na Najeriya, Mohammed Idris ya ce tattaunawarsu ta yi armashi sakamakon fahimtar da aka samu saboda Najeriya da Amurka sun yarda cewa idan za a samu zaman laiya tsakanin Isra'ila da Falasdinu, toh lalle ne a bar kowace kasa ta zauna a a matsayin mai cin gashin kanta.

Sai dai ya ce an samu banbanci kan halin da Gaza ke ciki saboda Najeriya ta fito karara ta nuna tana goyon bayan a dakatar da yaki amma Amurka "ba ta fito fili ta yi irin wannan magana kamar yadda ita Najeriya ta yi ba."

Halin da Nijar ta fada ciki bayan juyin mulki

A cewar Ambasada Tuggar, yanayin da Nijar take ciki batu ne da ya taso cikin tattaunawar manyan jami'an biyu.

"Dukkanmu mun yadda cewa juyin mulkin da aka yi ba daidai bane kuma za mu ci gaba da kokarin da aka saba yi, kamar yadda Najeriya take, kamar yadda Ecowas take da ita ma Amurka na ganin da farko an saki Shugaba Bazoum da iyalansa."

Ya ce a baya-bayan nan an saki ɗan Bazoum kuma "muna fata shi ma za a sake shi, sai kuma a cire takunkumai."

Taimaka wa Najeriya kan kalubalen tsaro da tattalin arziki

Ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Tuggar ya ce batun tsaro na cikin abubuwan da manyan jami'an suka tattauna kasancewar Amurka na da kimiyyar da ke taimaka wa wajen tsaro.

A nasa bangaren, Ministan yada labarai na Najeriya, Mohammed Idris ya ce Blinken ya yi magana a kan janye tallafin man fetur da shugaba Bola Tinubu ya yi. Tinubu kuma ya nemi Amurka ta shigo ta ba da taimako wajen samun tallafi a kasa ta yadda yan Najeriya ba za su shiga karin wahala ba.

Inganta Lafiya da noma a Najeriya

Ambasada Tuggar ya ce noma da abinci da magunguna da kuma yadda za a rika sarrafa su a Najeriya don tabbatar da cewa matasa sun samu aiki a masana'antu.

Ya yi magana kan irin noma wanda "kusan dama can irin a Afirka yake wanda ya bace amma su suna da shi wanda idan aka yi noma da shi ya fi iri na shinkafa da alkama na zamani." a cewarsa.

Ministan ya kara da cewa Amurka ta yi alkawarin bai wa Najeriya irin domin habaka amfanin gona a kasar.