Jihohin da INEC ta ce za a ci gaba da zaɓe ranar Lahadi

,
An wallafa

Yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya, za a iya cewa har yanzu zaune ba ta ƙare ba. Ganin cewa Hukumar zaɓen kasar ta ayyana wasu jihohi da ta ce za a sake zaɓen wasu mazaɓunsu, ko kuma za a ci gaba da gudanar da zaben.

Jinkiri da aka samu na kai kayan aikin zaɓe a wasu wuraren da kuma gaza aikin na'urar BVAS yadda ya kamata ya janyo kasa kammala zaɓen a kan lokaci a wasu wuraren.

A wasu yankunan kuma an riƙa samu matsalar hare-hare kan ma'aikatan zaɓen da kayan aikinsu, abin da ya hana kammala zaben, ita kuma hukumar zaɓe ta ce za a kammala a ranar Lahadi.

Jihar Bayelsa

A ranar Asabar ne Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ce ta ɗage zaɓe a wasu mazaɓu 141 a jihar Bayelsa da ke kudancin Najeriya.

Shugaban hukumar farfesa Mahmoud Yakubu ne ya bayyana hakan a jawabin da ya yi manema labarai a ɗakin tattaro sakamakon zaɓen 2023 da ke Abuja babban birnin Najeriya.

Ya ce an ɗage zaɓe a mazaɓun ne saboda tayar da rikici da wasu mutane suka yi.

Jihar Cross Rivers

A jihar Cross Rivers ma hukumar zaɓen ta bayyana matakin ci gaba da zaɓe a wasu yankuna, kasancewar ba a iya kammala zaɓen ba a ranar Asabar.

Sanarwar da hukumar ta fitar ta hannun jami'ar yaɗa labarun hukumar a jihar, Anthonia Nwobi, INEC ta ce za a yi zaɓen ne na ranar Lahadi a wasu rumfunan zaɓe a ƙaramar hukumar Bakassi

Jihar Taraba

Hukumar zaɓe a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya ta tabbatar da cewa za a ci gaba da zaɓe a jihar a yau Lahadi.

INEC ta tabbatar wa BBC cewa jihar Taraba na cikin jihohin da za a ci gaba da zaɓen.

Hakan dai ba ya rasa nasaba da rashin isar kayan zaɓe a kan lokaci zuwa wasu rumfunan zaɓen, kuma intanet ɗin na'urar BVAS na daukewa.

Haka kuma rahotonni sun ce an yi garkuwa da wasu ma'aikatan zaɓen na wucin-gadi guda uku a ƙaramar hukumar Donga.

Wani jami'in hukumar da ya buƙaci a sakaya sunansa ne ya bayyana wa BBC faruwar lamarin.

To sai dai jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar SP Usman Abdullahi ya ce suna kan gudanar da bincike domin gano yadda lamarin ya faru.

...
...

Jihar a Edo

Shugaban Hukumar Zaɓen Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu ya ce za a sake zaɓe a wasu mazaɓu na jihar Edo, bayan samun matsala ta rashin saka alamar wata jam'iyya a takardar kaɗa kuri'a a wasu mazaɓu biyu na jihar, ya sanya an ɗage zaben sai a ranar 11 ga watan Maris lokacin gudanar da zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisar dokokin jiha.

Ya ce za a yi haka ne saboda kowa doka ta ba shi damar yin zaɓe, don haka INEC za ta yi duk iyawarta na ganin tabbatuwar hakan.

Sannan ya ce a yau ne za a buɗe karɓan sakamakon zaɓen shugaban ƙasan Najeriya na 2023.

Jihar Kogi

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta soke zaɓe a wasu cibiyoyin zaɓe na mazaɓar Kogi ta Gabas sakamakon hargitsin da wasu ɓatagari suka haifar a wuraren.

A cewar INEC, an soke zaɓe a rumfunan zaɓe biyu a Nyigba sai wasu biyar a yankin Omala na jihar ta Kogi.

Hukumar zaɓen ta bayyana cewa ɓata-garin sun yi ta harbi a iska inda suka tarwatsa masu zaɓen, hakan a cewarta ya saɓa da dokar zaɓe kuma dole ta sa aka soke zaɓe a wuraren da lamarin ya faru.

INEC ta ce lamarin ya sa an dakatar da zaɓe ɓagatatan a rumfunan, amma ba ta bayyana cewa ko za a ci gaba da zaɓen ba a ranar Lahadi.

Mutane da dama sun riƙa nuna fushinsu kan wannan tsaiko da aka riƙa samu yayin zaɓukan.

A birnin Legas wasu masu zaɓe sun riƙa bayyana damuwarsu kan rashin kai musu kayan aiki a kan lokaci

G