An ga watan azumin Ramadan a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar na uku ya sanar da ganin jaririn watan Ramadan na shekarar 2023 a wasu sassan Najeriya.
A jawabin da ya yi na sanarwar wanda aka sanya a shafin Tuwita na kwamitin ganin watan, Sarkin Musulmin ya ce an ga watan ne bayan samun rahotanni daga shugabannin addinin Musulunci da ke wasu jihohin ƙasar.
Hakan na nufin ranar Alhamis 23 ga watan Maris din 2023 ne za ta kasance daya ga watan Ramadan.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X








