Ramadan: Mutanen da azumi ya wajaba a kansu da wadanda bai hau kansu ba

Bayanan bidiyo, Ramadan: Mutanen da azumi ya wajaba a kansu da wadanda bai hau kansu ba
An wallafa

Ku latsa bidiyon da ke sama domin kallon bidiyon:

Malaman addinin Musulunci sun bayyana mutanen da azumi ya hau kansu a yayin da watan Ramadana ya shiga kwana na shida.

Kazalika, malaman sun yi bayani kan mutanen da aka dauke wa azumin watan Ramadan.

Fitaccen malamin nan da ke Kaduna, Sheikh Halliru Maraya, ya shaida wa BBC cewa azumi ya wajaba kan Musulmi, baligi, mai hankali.

Hakan kuma azumi bai hau kan matafiyi ba da kuma mace mai jinin haila ko da yake daga baya za su rama.