Golan Man City Ederson zai yi jinyar mako hudu

Edreson

Asalin hoton, Reuters

An wallafa

Mai tsaron ragar Manchester City, Ederson zai yi jinyar mako hudu, bayan raunin da ya ji a wasan da suka tashi 1-1 da Liverpool ranar Lahadi a Anfield.

Ederson ya ji rauni ne bayan ketar da ya yiwa Darwin Nunez da ta kai an bai wa Liverpool fenariti, wanda ya bai wa kungiyar damar farke kwallon.

Koda yake dan kasar Brazil ya ci gaba da karawar bayan da aka duba lafiyarsa daga baya jikin ya yi tsami aka sauya shi da Stefan Ortega.

Ederson, mai shekara 30 ba zai buga wa City Premier League ba a gida da za ta karbi bakuncin Arsenal ranar 31 ga watan Maris.

Haka kuma ba zai yi wasan FA Cup ba zagayen daf da na kusa da na karshe a gida da Newcastle United.

City ta auna koshin lafiyar golan ta kuma sanar da Brazil cewar Ederson ba zai iya buga wa kasar wasannin sada zumunta ba.

Kenan Ortega, mai shekara 31 shi ne zai tsare ragar City ranar Laraba a wasa da Aston Villa 3 ga watan Afirilu da wanda za ta ziyarci Crystal Palace.