Arsenal na son Coman, Crystal Palace na zawarcin Rashford

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta tuntubi Bayern Munich kan dan wasanta Kingsley Coman, mai shekara 28. (Sky Sports)
Eintracht Frankfurt na duba yiwuwar saida dan wasa Hugo Ekitite mai shekara 22, kan kudi sama da fam miliyan 86, a daidai lokacin da kungiyoyin Arsenal da Tottenham ke zawarcin dan wasan. (Bild - in German)
A shirye Tottenham ta ke kan sayen dan wasan gaba na Wolves Matheus Cunha, mai shekara 25, kan kudi fam miliyan 65. (Fichajes - in Spanish)
Crystal Palace na son dauko dan wasan gaba na Manchester United, Marcus Rashford, mai shekara 27. (Sun)
Liverpool da Everton na son dan wasan tsakiya na Sunderland, Chris Rigg, 17, a kakar wasan nan. (The i)
Watakil Manchester United za ta saida mai tsaron raga Andre Onana, 29, a kakar nan, hakan zai sauya idan har za ta samu ribar fam miliyan 40 kan dan wasan (NBC Sports)
Harwayau, Manchester United ta rage farashin da ta sanyawa dan wasan gaba Alejandro Garnacho, 20, daga fam miliyan 50 zuwa fam miliyan 40, domin ganin ta saida shi kan lokaci. (Tutto Mercato Web - in Italian)
United na son matashin dan wasan Ajax Abdellah Ouazane, 16, bayan dan wasan tsakiyar ya fito cikin 'yan 17 da za su bugawa Morocco a gasar cikin kofin Afurka. (Daily Mail)
Manchester City za ta kara tsawaita kwantiragin dan wasan tsakiya Ilkay Gundogan, 34, har zuwa shekarar 2026. (Fabrizio Romano)
Real Madrid na son ɗan wasan gaban City, Erling Haaland, mai shekara 24, idan dan wasan gaban kulub din Vinicius Jr ya koma taka leda a kasar Saudiyya kamar yadda ake yada jita-jita. (Sky Sports)
Barcelona na son fam miliyan 78, kan dan wasa Raphinha, mai shekara 28, a daidai lokacin da ake yada jita-jitar dan wasan na son komawa Saudi Pro League. (Catalunya Radio - in Spanish)









