Coman ya maimaita cin PSG kamar yadda ya yi a 2020

Kingsley Coleman

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Bayern Munich ta je Faransa ta ci Paris St Germain 1-0 a wasan farko zagayen 'yan 16 a Champions League.

Kingsley Coman ne ya ci kwallo, shine ya ci PSG a wasan karshe a kakar 2020 da Bayern ta lashe Champions League.

An fara karawar da Lionel Messi daga baya Kylian Mbappe ya shiga wasan, amma sun kasa samun sakamakon da kungiyar ke bukata.

Mbappe ya zura kwallo a raga, amma a soketa da cewar an yi satar gida tun kan ta kai ga shiga raga.

PSG mai rike da Ligue 1 ta sha kashi a wasa uku a jere a dukkan karawar da ta yi kwanan nan.

Wasu karin bayanai kafin karawa tsakanin PSG da Bayern:

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Paris St Germain za ta fafata da Bayern Munich ranar Talata a wasan farko a Champions league zagayen kungiyoyi 16 da suka rage a gasar.

Bayern za ta buga wasan ne, bayan karawa 19 a jere ba a doke ta ba - har da lashe wasa uku da ta buga a bayan nan.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kungiyar Jamus ta kawo wannan matakin, bayan cin dukkan karawa shidan da ta yi a Champions League a kakar nan.

PSG da Bayern Munich sun sha haduwa a zagayen 'yan 16 a Champions League.

Kaka ta 11 da PSG ke zuwa matakin 'yan 16 a gasar zakarun Turai, Real Madrid da Bayern ne ke gabanta a wannan kwazon.

Rabon da Bayern ta kasa zuwa irin wannan matakin tun kakar 2007/08, ita kuwa Real kan je zagayen 'yan 16 tun da aka kirkiro gurbin a 2003/04

Sai dai karo hudu ana fitar da PSG daga wasa shida baya a zangon 'yan 16, ita kuwa Bayern sau daya ta kasa kai wa Quarter final daga fafatawa 10 a baya shine a 2018/19.

Bayern ta ziyarci Faransa ba tare da Sadio Mane da Lucas Hernández da Noussair Mazraoui da kuma Manuel Neuer, wadanda ke jinya.

Ryan Gravenberch ya warke, bayan da bai yi mata karawa da Wolfsburg da Bochum ba, Joshua Kimmich zai buga fafatawar, bayan dakatar da shi a Bundesliga.

Kylian Mbappe wanda ya ci kwallo bakwai a cikin rukuni a Champions League a bana ya murmure, wanda aka ce zai yi jinya mai tsawo tun farko.

Kyaftin din Argentina, Lionel Messi yana cikin 'yan kwallon da PSG ta bayyana da za su kara da Bayern ranar Talata.

Tsohon dan kwallon Bayern, Renato Sanches wanda ke taka leda a PSG na yin jinya.

Kungiyoyin sun kara a Champions League sau 11, inda PSG ta ci karawa shida, ita kuwa Bayern ta yi nasara a biyar.

Wasa 11 baya da aka kara tsakanin kungiyoyin biyu:

2020/2021

Champions League

  • Paris St-G. 0 - 1 Bayern Munich

Champions League

  • Bayern Munich 2 - 3 Paris St-G.

2019/2020

Champions League

  • Paris St-G. 0 - 1 Bayern Munich

2017/2018

Champions League

  • Bayern Munich 3 - 1 Paris St-G.

Champions League

  • Paris St-G. 3 - 0 Bayern Munich

2000/2001

Champions League

  • Bayern Munich 2 - 0 Paris St-G.

Champions League

  • Paris St-G. 1 - 0 Bayern Munich

1997/1998

Champions League

  • Paris St-G. 3 - 1 Bayern Munich

Champions League

  • Bayern Munich 5 - 1 Paris St-G.

1994/1995

Champions League

  • Bayern Munich 0 - 1 Paris St-G.

Champions League

  • Paris St-G. 2 - 0 Bayern Munich