DSS ta musanta kai samame wani gida a Abuja tare da sojojin Amurka

Bichi DSS

Asalin hoton, DSS

An wallafa

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta Najeriya ta yi watsi da labarin da ke cewa jami’anta ƙarƙashin hadin gwiwar sojojin Amurka sun kai samame wani gida a Abuja, babban birnin ƙasar.

Mai magana da yawun hukumar Dr. Peter Afunanya ne ya tabbatar wa kafofin yaɗa labarai wannan batu a ranar Juma’a.

Rahotanni sun fara yaɗuwa a farkon wannan makon cewa jami’an DSS da sojojin Amurkan sun kai samamen ne wani gida a unguwar Lugbe inda suka kama wasu mutane da ake zargin ƴan Boko Haram ne tare da abubuwan fashewa da dama.

Hakan na zuwa ne bayan da a farkon makon nan Amurkan ta fitar da sanarwa tana gargaɗin cewa akwai yiwuwar za a kai hare-haren ta’addanci a sassan Najeriya musamman Abuja.

Amma tuni gwamnatin Najeriya ta yi watsi da wannan batu na Amurka tana mai kiran ƴan ƙasar su kwantar da hankulansu.

Sai dai hakan bai hana Amurka ci gaba da kiraye-kirayen ba, tana mai umartar ƴan ƙasarta mazauna Najeriya da su bar ƙasar.

Kafar yaɗa labaran PR Nigeria ta ruwaito Dr Afunanya yana cewa “Ina shaida mkuku cewa babu wani samame da muka kai tare da sojojin Amurka kamar yadda ake yaɗawa.

“Duk da cewa dai mun kai samame wani rukunun gidaje a Abuja tare da sauran hukumomi abokan aiki, to babu dakarun tsaron ƙasashen waje ko ɗaya a ciki,” ya ce.

PR Nigeria ta ce a wani binciken ƙwaf da ta aiwatar kan zargin dakarun ƙasashen waje sun kai samame rukunin gidaje na Trademore, ya gano cewa “babu wasu ƙwararan hujjoji cewa sojojin Amurka sun kama wani a Abuja.

Me yake faruwa a Abuja

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tun bayan samun labarin kai samamen jami'an tsaron da aka yaɗa, hankulan mazauna Abuja suka sake tashi na rashin sanin tabbas kan abin da ka iya faruwa.

Kazalika ƙarin ƙasashe biyar sun bi sahun Amurka da Birtaniya wajen bayyana fargabar kai harin ta'addanci a Abuja babban birnin Najeriya tun daga ƙarshen makon da ya gabata, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Amurka ce ta fara bayyana damuwa a ranar Lahadi, tana mai cewa akwai yiwuwar kai hari kan gine-ginen gwamnati da wuraren taruwar jama'a, kafin a ranar Juma'a ta umarci wasu ma'aikatan difilomasiyyarta su fice daga binin tare da iyalansu nan take.

Jim kaɗan bayan haka Ofishin Harkokin Waje na Birtaniya ma ya gargaɗi 'yan ƙasarsa da su ankare kuma su guji yawo a Abuja tare da kauce wa shiga taron jama'a.

Ƙasashen Jamus da Bulgeriya da Ireland da Kanada da Denmark sun bi sahu, inda suke cewa akwai yiwuwar 'yan ta'adda za su kai hare-hare sannan suka nemi 'yan ƙasashensu su yi taka-tsantsan ko kuma su fice daga birnin.

Sai dai Babban Sufeton 'Yan Sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba ya jaddada cewa babu wata fargabar kai hare-hare a Abuja, bayan ya umarci jami'ansa da su tsaurara tsaro a kewayen Abuja.

"Saboda haka IGP na kwantar wa da mazauna Abuja hankali tare da ƙarfafa musu gwiwar ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum yayin da aka shirya tsafi don daƙile barazanar tsaro da kuma amsa kiran gaggawa a kan lokaci," in ji sanarwar da kakakin 'yan sandan ya fitar ranar Alhamis.

Me gwamnatin Najeriya ta ce?

Lai Mohammed

Asalin hoton, NG

A ranar Laraba 26 ga watan Oktoba ma gwamnatin Najeriya ta nuna ɓacin ranta game da jerin gargaɗin da ofishin jakadancin Amurkar a Najeriya ke fitarwa kan barazanar kai hare-haren.

A martanin da ta mayar ta bakin ministan yaɗa labaru Lai Mohammed, ranar Laraba, a Abuja, gwamnatin Najeriya ta ce mazauna Abuja da ma sauran yankunan ƙasar ba su cikin haɗari.

Lai Mohammed ya ce “Ina tabbatar wa al’ummar Najeriya da na ƙasashen waje da suke zaune a Najeriya cewa jam’ian tsaro na bakin ƙoƙarinsu kan matsalar tsaro”.

Ya ƙara da cewa “babu wata barazana, kuma babu baƙatar wani ya tayar da hankalinsa.”

Ministan ya ce ba Najeriya ce kawai take fama da matsalar tsaro ba, kasancewar kowace ƙasa na da irin nata matsalar tsaron da take fuskanta.

Inda ya kafa hujja da hare-haren da ɗaiɗaikun ƴan bindiga ke kai wa a makarantun Amurka.

Abin da Shugaba Buhari ya ce

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shawarci hukumoin tsaron ƙasar da dukkan al’umma da su ci gaba da yin taka tsantsan da kula kan sha’anin tsaro, amma kuma ya ce yana da matuƙar muhimmanci a guji tayar da hankula.

A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar a yau Juma’a, shugaban ya nemi ƴan ƙasar da su kwantar da hankali. “Sabbin matakan barin ƙasar da Amurka da Birtaniya ke ɗauka ba za su zama dalilan tayar da hankali ba.”

Shugaba Buhari

Asalin hoton, Presidency

Wannan magana ta shugaban ƙasar na zuwa ne a yayin da hankula ke ci gaba da tashi kan batun tsaro a Najeriya, tun bayan gargaɗin da Amurka da wasu ƙasashen yamma suka yi cewa akwai yiwuwar kai hare-haren ta’addanci a ƙasar.

“Najeriya ba ita kaɗai ce ƙasashen duniya ke bai yi wa gargadi kan barazanar ta’addanci da kuma bai wa ƴan ƙasashensu shawarar tafiye-tafiye ba.

Amurka da Birtaniya na kuma yin gargaɗi kan yiwuwar hare-hare a ƙasashen yammacin Turai. Sannan sun bai wa ƴan ƙasarsu irin shawarwarin da suka fitar a Najeriyar.

“Abin takaici ne cewa batun ta’addanci ya mamaye duniya.

Sanarwar ta ci gaba da cewa sai dai gargaɗin ba yana nufin lallai za a kai hare-haren ba, don tun bayan harin daka kai gidan yarin Kuje an sake tsaurara tsaro a ciki da wajen Abuja.

“An daƙile hare-hare. Jami’an tsaro ne bankaɗo barazanar da ake fuskanta don tsaron ƴan ƙasa – sai dai mafi yawan ayyukansu ba a gani saboda ana buƙatar sirri.

“Zaman lafiyar ƴan Najeriya shi ne mafi ƙololuwar burin gwamnati. Jami’an tsaro na aiki babu dare babu rana,” in ji sanarwar.

Kazalika shugaban ƙasar ya bayar da tabbacin cewa gwamnati na bakin ƙoƙarinta wajen tabbatar da tsaro.