Arsenal na nazari kan Rogers,Marseille na zawarcin Tsimikas

Morgan Rogers

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Morgan Rogers
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Arsenal na nazari kan tayin da za ta gabatarwa ɗan wasan tsakiyar Ingila Morgan Rogers, mai shekara 23, amma Aston Villa na son kudi da ba zai yi kasa da fan miliyan 80 ba.(Sun), external

RB Leipzig ta cimma matsaya da Liverpool kan ɗan wasan tsakiya na tawagar Ingila 'yan kasa da shekaru 21, Harvey Elliott, mai shekara 22, yayin da ɗan wasan tsakiya na Netherland Xavi Simons mai shekara 22, na gab da komawa Chelsea. (Florian Plettenberg), external

Marseille na son ta dauko ɗan wasan baya na ƙasar Girka Kostas Tsimikas mai shekara 29 , wanda ake sa ran zai bar Liverpool a wannan bazara. (Footmercato - in French), external

Dan wasan mai kai hari na Manchester United da Denmark Rasmus Hojlund, mai shekara 22, da wakilansa sun fito karara sun faɗawa Napoli da RB Leipzig cewa ya fi son a bada shi aro sannan a saye shi . (Fabrizio Romano), external

Nottingham Forest na tattaunawa don siyan ɗan wasan bayan Sevilla ɗan kasar Sfaniya Jose Angel Carmona mai shekaru 23.(Sky Sports), external

Forest kuma na nazarin yiwuwar sake haduwa da mai tsaron baya na ƙasar Poland da Aston Villa , Matty Cash mai shekara 28.(Athletic - subscription required), external

Har yanzu Everton na son siyan sabbin 'yan wasa kafin wa'adin karshe - musamman ɗan wasan gefe - kuma za ta iya sake yin wani tayin neman ɗan wasan gaban Southampton da Ingila Tyler Dibling, mai shekara 19.(Sky Sports), external

Dan wasan baya na Aston Villa da Sfaniya Alex Moreno, mai shekara 32, na gab da komawa Girona bayan ya amince ya rage ƙudin da zaa biya shi. (Athletic - subscription required), external

Tottenham ta kara kaimi a kokarin dauko ɗan wasan baya na Brentford da Ireland Nathan Collins, mai shekara 24, wanda shi ma Liverpool ke zawarcinsa. (Caught Offside), external

Bournemouth ta fara tattaunawa da Chelsea kan ɗan wasan baya na Faransa Axel Disasi, mai shekara 27. (Sacha Tavolieri via Football Insider)