Man Utd na nazari kan Wharton, Da alama zaman Onana ya zo karshe a Utd

Adam Wharton

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United na nazari kan miƙa tayinta kan ɗan wasan tsakiya a Crystal Palace da Ingila, Adam Wharton mai shekara 21. (Talksport)

Inter Milan tayi watsi da tayin yuro miliyan 50 daga Chelsea kan ɗan wasanta na Italiya, Alessandro Bastoni mai shekara 26. (La Gazzetta dello Sport)

Ɗan wasan tsakiya a RB Leipzig da Netherlands, Xavi Simons mai shekara 22, ya faɗawa ƙungiyarsa yana son zuwa Chelsea, duk da tayin da yake samu daga Bayern Munich da Manchester City. (ESPN)

AC Milan ta matsa ƙaimi kan saye ɗan wasan Denmark da Manchester United, Rasmus Hojlund mai shekara 22 kan yuro miliyan 35, sai dai kuma tana nazari kan ɗan wasan gaba a Juventus da Serbia, Dusan Vlahovic mai shekara 25. (La Gazzetta dello Sport)

Ɗan wasan Manchester City da Ingila, Rico Lewis mai shekara 20, ya ce bashi da niyyar barin ƙungiyar duk da zawarcinsa da Nottingham Forest ke yi. (Mail)

Mai tsaron raga a Kamaru Andre Onana mai shekara 29, ya sha zaman benci a fafatawar Manchester United a soma Firimiyar Ingila da ta haska da Arsenal, yanayin da ke tabbatar da yunƙurin ƙungiyar na neman dawo da David de Gea mai shekara 34 daga Fiorentina. (Sun)

Sai dai, United a yanzu ta sa kuɗaɗenta a neman mai tsaron raga na Aston Villa da Argentina, Emiliano Martinez mai shekara 32, da kuma ɗan wasan Paris St-Germain da Italiya, Gianluigi Donnarumma, mai shekara 26. (Telegraph - subscription required)

Albashin Jadon Sancho ya kasance abin da ya ke nazari a tafiyarsa Roma daga Manchester United. Ɗan wasan mai shekara 25 daga Ingila na son ganin ko akwai ƙungiyoyin da za su iya bashi abin da ya ke samu duk mako wato £250,000. (Teamtalk)

Roma ita ma ta tuntuɓi Manchester United kan yarjejeniya da ɗan wasan Netherlands mai shekara 26, Tyrell Malacia, wanda Besiktas ke zawarci. (Fabrizio Romano)

Atalanta na fatan cimma yarjejeniya da Fulham kan ɗan wasan gaba a Brazil, Rodrigo Muniz mai shekara 24, kan yuro miliyan 40. (Teamtalk)

Ɗan wasan gaba a Faransa, Randal Kolo Muani mai shekara 26, ya amince da ya rage albashinsa domin komawa Juventus daga Paris St-Germain, a yarjejeniyar yuro miliyan 60. (Corriere dello Sport in Italian)

Tottenham na nazari kan ɗan wasan nan mai shekara 24 daga Real Sociedad da Japan, Takefusa Kubo yayinda Thomas Frank ke kokarin raba kafa. (Fichajes - in Spanish)

Burnley da Sunderland kowanne na son ɗan wasan FC Copenhagen da Brazil Gabriel Pereira mai shekara 25. (Teamtalk)

Arsenal na son ɗauko ɗan wasan tsakiya a Barcelona, Frenkie de Jong mai shekara 28. (Fichajes - in Spanish)