Ko ratar da ke tsakanin ƴan Najeriya mazauna ƙasar waje da na cikin gida na ƙaruwa?

Asalin hoton, The Plug Entertainment
- Marubuci, Danai Nesta Kupemba
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Yadda ake ake hada-hada a Najeriya a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara wani abu ne tamkar a shirin fim: haɗuwa da juna cikin shauƙi a filayen jiragen sama da bukukuwan shagali da kalankuwar mawaƙa da sauran su.
A lokacin ne ƴan Najeriya da ke zaune a ƙasashen waje ke ziyartar gida. Ana musu laƙabi da IJGB wato 'I Just Got Back' da Ingilishi.
Za ka ji su suna magana da karyayyen harshe irin ta turawa a tsakiyar masu magana da turancin buroka na Najeriya da ake kira Pidgin. Suna zuwa da kuɗaɗen kashewa na ƙasashen waje.
Amma lamarin na ƙara fito da wani yanayi maras daɗin ji.
Waɗanda suke rayuwa a cikin Najeriya, suke samun albashi ko ladar aikinsu da naira, suna wahala, musamman a birane irin su Legas da Abuja saboda hauhawar farashin kayayyaki a lokacin ƙarshen shekara.
Mazauna suna kiran lokacin da "Detty December", domin nuna yanayin da ake kasancewa a lokutan bukukuwan kirsimeti da ƙarshen shekara.
Lokacin bukukuwan ƙarshen shekara, komai a Legas yana canjawa - farashin kayayyaki suna tashi, sannan kwastomomi sukan daina hulɗa da asalin kwastomominsa, kamar yadda wani ɗanjarida na bayyana wa BBC.
Da gaske ne duk da cewa Najeriya mai arzikin man fetur ita ce ta fi kowace ƙasa arziki a Afirka, mutanenta kusan miliyan 230 suna fuskantar ƙalubalen rayuwa da dama.
A farkon wannan shekarar, gidauniyar Oxfam ta yi gargaɗin cewa ratar arzikin da ke tsakanin masu kuɗi da talakawa a Najeriya, "ya kai maƙura."
Alƙaluman 2023 suna tayar da hankali. A cewar alƙaluman cibiyar World Inequality Database, kusan kashi 10 na ƴan ƙasar ne suke riƙe da sama da kashi 60 na arzikin ƙasar.
Sannan bankin duniya ya ce waɗanda suke rayuwa cikin talauci a ƙasar sun kai miliyan 87, inda ta zama "ƙasa ta biyu da ta fi yawan matalauta a duniya bayan India."

Asalin hoton, AFP
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Martins Ifeanacho, farfesan sanin halayyar ɗan'adam ne a Jami'ar Fatakwal, ya ce ratar da ke tsakanin masu kuɗi da matalauta ƙaruwa take yi tun bayan samun ƴancin kai daga Birtaniya a 1960.
"Muna fama da matsin tattalin arziki," inji malamin, wanda ya koma Najeriya bayan ya yi karatu a Ireland a shekarun 1990s.
Ya ce rashin wadatar zuci ta masu riƙe da madafun iko a ƙasar ce ta ƙara jefa talakawan ƙasar cikin talauci.
A wajen cin abinci, waɗanda suka zo da motoci manya irin su Range Rover ake fara sayarwa abincin, kafin masu ƙananan motoci irin su Kia.
Bankin duniya ya ce "rashin samar da aikin yi da inganta harkokin kasuwanci," ne suke kawo tsaiko wajen samar da aiki ga "kusan ƴan Najeriya miliyan 3.5 da suke shiga sahun masu neman aiki a duk shekara."
Wannan ya sa ƴan ƙasar da dama suke neman ficewa daga ƙasar zuwa wasu ƙasashen da suke tunanin samun rayuwa mai kyau.
Ficewar ake kira da "japa", daga kalmar yaren Yarbanci mai nufin "tserewa."

Asalin hoton, Getty Images
Wani bincike da aka yi a shekarar 2022 ya gano cewa aƙalla kashi 70 na matasan ƙasar suna da burin ficewa daga ƙasar.
Amma kuma ficewar ga wasu na da wahala. Fita karatu, wanda ta fi zama hanya mai sauƙi kuma na buƙatar dubban daloli.
"Japa ya sa yanzu matasa da dama burinsu kawai su bar ƙasar nan," in ji wata jami'ar ɗaukar aiki mai suna Lulu Okwara mai shekara 28.
Ta yi karatu ne a Birtaniya, amma ta zo Najeriya aƙalla sau uku.
Ta ce a Najeriya ana neman samun nasarar rayuwa ko ta halin ƙaƙa, wanda a cewarta hakan ya sa mutane suke tunanin za su iya yin komai domin samun nasara.
Amfani da harshe irin na Turawa zai iya taimakonka wajen sauƙin samun nasara a Najeriya - ko da kuwa ba ka taɓa zuwa turai ba.
"Wannan ya sa wasu suke ƙaryar karyar harshe kamar turawan Birtaniya saboda a girmama su," in ji Farfesa Ifeanacho.

Asalin hoton, Getty Images
Amfani da harshe tamkar na Amurka ko Birtaniya na taimakawa wajendaga martabar mutum.
Bizzle Osikoya, shugaban kamfanin The Plug Entertainment, mai shirya tarukan kalankuwa a Afirka ta Yamma ya ce yakan fuskanci irin wannan matsalar ta mutanen da suka zo daga turai, suka bayar da kuɗi, sai kuma can su janye kuɗaɗensu.
A Najeriya, yadda mutum ya bayyana kansa yana da matuƙar muhimmanci - sannan waɗanda suka koma gida Najeriya daga ƙasashen wajen waɗanda suka bayyana isarsu, su ne za su fi samun daraja.











