Kudi ne ke kai 'yan wasa Saudiyya-Ibrahimovic

Asalin hoton, Getty Images
Zlatan Ibrahimovic ya ce 'yan wasan kwallon kafa da suka koma Saudiyya sun mayar da harkar wasanninsu, wani al'amari na ne kudi kawai maimakon nuna hazakar da suke da ita.
Dan kasar Sweden din, mai shekara 42, ya yi ritaya ne daga fagen kwallon kafa a watan Yuni a kulob din AC Milan, bayan ya lashe gasanni masu yawa lokacin da yake wasa.
Tsohon dan wasan na Manchester United da Paris St-Germain, ya ce ya samu tayin zuwa China da Saudiyya don buga kwallo, amma duka ya yi watsi da su.
A wata hira da Piers Morgan, Ibrahimovic ya ce "Na samu tayi daga China da kuma Saudiyya," in ji shi "Amma halin da ake ciki shi ne, wani buri kake da shi? Wadanne manufofi kake son ka cimma?
“Zai fi dacewa a tuna da kai don hazakarka, ba don kudin da ka tara ba''.
Manyan ‘yan wasan da suka hada da Cristiano Ronaldo da Riyad Mahrez da Karim Benzema da dan wasan tsakiya na Ingila Jordan Henderson sun koma Saudiyya cikin watanni 12 da suka wuce.
Bayan ya shafe lokaci yana taka leda a kungiyoyi da dama na Turai, Ibrahimovic ya koma LA Galaxy ta MLS daga United a 2018, kafin ya dawo AC Milan a karo na biyu, inda ya taimaka musu lashe gasar Seirie A a kakar wasan 2021-22.
Gasar Saudi Pro League ta fara jan hankalin 'yan wasa tun daga farkon shekarar 2023, lokacin da asusun Zuba Jari na Kasar (PIF) mallakar Newcastle United, ya karbe hudu daga cikin manyan kungiyoyin gasar - Al-Ahli da Al-Ittihad da Al-Hilal da kuma Al-Nassr.











