Waiwaye: Komawar Tinubu Najeriya da kwaso ɗalibai daga Sudan
Wannan maƙala ce da ke tattaro muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi
Tinubu ya koma Najeriya bayan hutu a Paris

Asalin hoton, Bola Ahmed Tinubu/Twitter
A farkon makon da muke bakwana da shi ne, zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya koma ƙasar, bayan wata ziyarar hutu da ya yi a ƙasar Faransa inda ya shafe tsawon mako biyar.
Tinubu ya sauka ne da yammacin Litinin a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, da ke Abuja babban birnin ƙasar.
Magoya bayan zaɓaɓɓen shugaban ƙasar da manyan jiga-jigai a jam'iyyar APC mai mulki, ciki har da zaɓaɓɓen mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ne suka tarbe shi lokacin da ya sauka a filin jirgin.
Gwamnatin Najeriya ta damu kan halin da 'yan ƙasar ke ciki a Sudan

Asalin hoton, Buhari Sallau
Gwamnatin Najeriya ta ce jami'anta na iya bakin ƙoƙarinsu da haɗin gwiwar ofishin jakadancin ƙasar a Sudan, da gwamnatocin ƙasashen Sudan da Habasha domin tabbatar da kare lafiyar dubban 'yan ƙasar da ke can.
Cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar, jami'ai sun yi ƙarin haske kan halin da ake ciki game da ɗaliban Najeriyar da rikicin Sudan ya ritsa da su.
Sanarwar ta shawarci waɗanda za a kwaso su tsaya a inda aka umarce su, da kayan da za su iya riƙewa a hannu kawai. Kuma kada su yi amfani da bayanan da ke yawo a kafafen sada zumunta.
Sanarwar ta ce wakilan ofishin jakadancin Najeriya za su kasance a Khartoum domin tabbatar da kwashe ɗaliban da sauran 'yan Najeriyar da ke birnin.
An kuma ba da shawara su tanadi takardunsu na shigi da fice, ta yadda idan sun je kan iyakar Masar, ba za a sha wuyar tantance su ba.
Tun da farko, sanarwar ta ambato cewa an kwashe mutum 637 daga Khartoum cikin motoci 13, waɗanda ta ce a halin da ake ciki suna kan iyakar Masar ana tantance su.
‘Yan sanda sun fara farautar shugaban INEC na Adamawa Hudu Ari

A makon da ya gabatan ne kuma, Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya umurci wani ayarin 'yan sanda ya yi aiki da hukumar zaɓen ƙasar wajen bincike da kuma tabbatar da ganin an gurfanar da shugaban hukumar zaɓe na jihar Adamawa da aka dakatar, Hudu Yunusa Ari a gaban kotu.
A wata sanarwar da kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi ya fitar, babban sufeton ya ce 'yan sanda za su tabbatar sun yi dukkan mai yiwuwa don gano dalilin da ya sa Hudu aikata abin da ya yi.
Ana tsaka da tattara sakamakon zaɓen gwamna a jihar Adamawa da aka ƙarasa ne, sai kwatsam Hudu Ari wanda shi ne kwamishinan zaɓe, ya ayyana Sanata Aishatu Binani ta APC a matsayin wadda ta lashe zaɓen.
IGP Usman ya ce a shirye suke su tabbatar da ganin doka ta yi aiki a kan duk waɗanda aka samu da hannu a lamarin na Adamawa, domin martaba dokokin ƙasa da tsarin dimokradiyya.
Ci-da-zucin 'yan adawa ne ya kayar da su zaɓe - Buhari

Asalin hoton, Buhari Sallau
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya yi imani ci-da-zuci ne babban abin da ya janyo taron 'yan adawar Najeriya suka sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa da ya wuce.
Ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi gwamnonin jam'iyyarsa ta APC a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi.
Yana cewa a daidai lokacin da jam'iyya mai mulki take aiki tuƙuru don ci gaba da mulki a zaɓukan da aka yi a baya-bayan nan, 'yan adawa suna can sun cika da ci-da-zuci.
"Sun je suna ta faɗa wa masu goya musu baya a ƙasashen waje cewa, sai sun kayar da APC.
Matawalle ya mayar da Sarkin da ya naɗa 'ƙasurgumin ɗan fashi' sarauta

Asalin hoton, ZAMFARA GOVNOR BELLO MATAWALLE/FACEBOOK
Haka kuma a dai cikin makon da muke bankwana da shi ɗin ne, gwamnan jihar Zamfara Muhammed Bello Matawalle, ya mayar wa Alh. Aliyu Garba Marafa sarautarsa ta Sarkin Birnin Yandoto.
A watan Yulin shekarar da ta gabata ne, gwamnan ya dakatar da sarkin ne saboda naɗa jagoran 'yan fashin daji, Ado Aleiru sarautar sarkin Fulani a fadarsa.
Naɗin da ya janyo ce-ce-ku-ce a ciki da wajen jihar.
A cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin Zamfara, Kabiru Balarabe Sardauna ya fitar, gwamnatin jihar ta tabbatar da mayar da sarkin kan karagarsa.
Ta ce an mayar da sarkin ne saboda buƙatar hakan da kwamitin da gwamnati ta kafa ya yi bayan kammala bincike kan lamarin.










