Muna son kasashen duniya su saka wa filayensu sunan Pele- FIFA

Asalin hoton, OTHER
Dubban masu makoki ne suka hallara a filin wasan Santos na Brazil, don ganawa da gawar tsohon dan wasan duniya Pele.
An ajiye gawar Pele a tsakiyar filin Urbano Caldiera da ke Sao Paulo, yayin da magoya baya suka yi dogon layi suna tozali da ita.
Tsohon dan wasan wanda ya kafa tarihin cin kofin duniya sau uku a tarihi, ya mutu ne ranar Alhamis yana da shekara 82.
Bayan mutuwar Pele ne gwamnatin Brazil ta ayyana makokin kwana uku.
Tun a 2021 ne aka gano cewa yana dauke da cutar kansa, kuma ya rika shige da fice asibiti saboda jinya.

Asalin hoton, Getty Images
Daga cikin manyan bakin da ke halartar jana'izar akwai shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Gianni Infantino, wanda yace za su bukaci ''kowace kasa a duniya ta saka sunan Pele a daya daga cikin filayenta.''







