Al Nassr: Za a gabatar da Ronaldo ga magoya baya

Asalin hoton, OTHER
Kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr ta Saudiyya za ta gabatar da sabon dan wasan gabanta Cristiano Ronaldo ga dubban magoya bayanta gobe Talata.
Al Nassr ta sayi kyaftin din na Portugal sama da yuro miliyan 200, bayan an yi baram-baram da tsohuwar kungiyarsa Manchester United.
Sau biyar Ronaldo na lashe kambun dan wasan duniya na Ballon d'Or, duk da burinsa na lashe kofin duniya a bana bai cika ba.
Tsohon dan wasan na duniya zai bayyana a filin wasan Al Nassr na Mrsool da ke Riyard da karfe 7:00 na yamma agogon Saudiyya.
Ronaldo zai samu kusan fam miliyan 173 a yarjejeniyar da ya kulla da kungiyar.
Itace yarjejeniya mafi tsada da aka taba kullawa da wani dan wasa a tarihi.
Ana sa ran magoya bayan Al Nassr su cika fili sosai don yin tozali da Cristiano Ronaldo.
Kwantiragin dan wasan za ta kare a watan Yunin 2025.











