Ciwon zuciya ya tilasta wa dan bayan Brighton yin ritaya

Enock Mwepu

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

An tilasta wa dan bayan kungiyar Brighton Enock Mwepe mai shekaru 24 murabus daga kwallon kafa saboda ciwon zuciya.

Kulob din na Premier ya ce Mwepu "yana fuskantar mummunan hadarin bugun zuciya" idan ya ci gaba da buga tamaula.

A baya-bayan nan Mwepu ya kamu da rashin lafiya yayin da yake kan kanyar zuwa Mali tare da kungiyar kwallon kafa ta Zambia.

Bai iya yin atisaye ba a kasar ta yammacin Afirka a watan jiya, kuma ya shafe kwana hudu a asibiti.

An yi wa Mwepu gwaji bayan ya koma Ingila sannan Brighton ya ce sakamakon ya nuna cewa" zabi daya kawai da yake da shi shi ne" ya yi murabus.

"Wadannan gwaje-gwajen sun tabbatar da cewa yana fama da matsalar ciwon zuciya ne na gado, wacce ta bayyana daga baya a rayuwarsa, sannan a baya babu wani abu da ya nuna cewa yana ganin likitan zuciya," kamar yadda Brighton ya fada a cikin wata sanarwa.

Mwepu ya ce zai yi murabus cikin "takaici", yana mai cewa ya cika burinsa na taka leda a gasar Premier, sai dai "wasu daga cikin mafarkan na sa sun zo karshe".

Sai dai ya kara da cewa "ba wannan ne karshen harkokina a kwallon kafa ba, na yi yunkurin shiga cikin harkokin wasanni a wasu matakan," kamar yadda ya fada a wata sanarwa a twitter.

Kwararren dan wasan ya koma kungiyar Brighton ne daga kungiyar Red Bull Salzburg a wata yarjejeniya ta shekara hudu, kuma an saye shi ne a kan kudi £18m (fam miliyan 18) a wayan Yulin 2021.

Ya ci wa kungiyar ta Brighton kwallo uku a wasanni 27 da ya buga, kuma wasansa na karshe shi ne wanda ya buga suka samu nasarar 5-2 a kan kungiyar Leicester City a watan Satumba.

Wasan Mwepu na na karshe shi ne wanda ya buga shi ne wanda suka samu nasarar 5-2 a kan kungiyar  Leicester City a watan Satumba.

Asalin hoton, Getty Images