Adadin wadanda suka rasu sakamakon arangama a sansanonin MDD a Dimokraɗiyar Congo ya kai 19

Asalin hoton, Reuters
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa har yanzu babu wata ƙwaƙƙwarar hujja da ke nuna cewa jami'anta na wanzar da zaman lafiya sun harbi farar hula a lokacin da ake gudanar zanga-zanga ta kwana uku kan jami'anta da ke Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo.
A halin yanzu, mutum 19 ne aka tabbatar da sun riga mu gidan gaskiya a yayin arangama daban-daban da aka yi a wasu garuruwan ƙasar inda aka kai hari ga sansanonin majalisar. Cikin waɗanda suka rasu sakamakon wannan arangamar har da jami'ai uku na Majalisar Dinkin Duniya.
An soma zanga-zangar ne tun a ranar Litinin a Gabashin Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo inda jama'a suka rinƙa zargin Majalisar Dinkin Duniya da gazawa wurin shawo kan rikice-rikicen da ƴan bindiga a ƙasar ke haddasawa.
Mataimakin wakili na musamman da Majalisar Dinkin Duniya ta aika Dimokraɗiyyar Congo ya ce tuni aka tura masu bincike domin taimaka wa hukumomin ƙasar tantance harsasen da suka kashe farar hula a garuruwan Goma da Butembo.
Mista Kassim Diagne ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa jami'an wanzanar da zaman lafiya sun kame kansu inda suka ƙi biye wa masu zanga-zangar a lokacin da suka afka sansanoninsu har suka ƙona motoci da ofisoshi tare da satar abinci.
Masu zanga-zangar sun zargi jami'an tsaro na ƙasar Congo da buɗe musu wuta.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da adadin farar hular da suka mutu ya ƙaru bayan wasu mutum huɗu daga cikin masu zanga-zangar wutar lantarki ta kashe su sakamakon harbin da jami'an tsaron ƙasar suka yi wanda harbin bindigar ya kakkaɓo wayar wuta daga turken lantarki inda ta faɗa kan masu zanga-zangar.
Kwamitin tsaro na majalisar dai ya yi Allah-wadai da wannan rikici inda ya buƙaci gwamnatin Congo ta gudanar da cikakken bincike tare da ɗaukar mataki kan waɗanda aka samu da laifi. Shirin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya a Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo shi ne na biyu mafi girma a duniya, sai dai a ƴan shekarun nan ya rinƙa janye dakarunsa daga wasu sassan ƙasar.











