Abdullahi Shehu Academy ta lashe marakin gasar sallah

Shehu Academy ta lashe maraki a gasar da dan kwallon Super Eagles, Abdullahi Shehu ke gudanarwa a kowacce babbar sallah a jihar Sokoto, Najeriya.
Shehu Academy ta yi nasarar doke Dambuwa Strikers da ci 3-0 a wasan karshe da suka kara a Giginya Memorial stadium.
Gasar dai ta falle biyu ce wato ajin gwanaye ta Premier Division da kuma ajin kwararru ta Professional Division.


A ajin gwanaye wato premier shi ne kungiyar Shehu Academy ce ta lashe marakin da kuma kofi .
Gabanin wannan karawar an buga wasan karshe ta fallen gasar ajin kwararrun tsakanin Nagarta FC da Sokoto youth Academy inda Nagarta FC ta lashe maraki da ci 2-1.
Mawakin nan dan asalin jihar Sokoto Usman Umar Soldier Boy, shi ne ya dauki nauyin kawo marakin a wannan matakin.
Kungiyoyin da suka zo na biyu dai sun samu kyautar raguna kowace. Yayinda wadanda suka fi saka kwallo raga suka samu kyautar bunsurai.
Kungiyoyi 21 ne suka fafata a gasar matakin premier yayinda 40 suka buga professional duk a cikin makonni biyu.












