Joe Gomez zai ci gaba da taka leda a Liverpool

Joe Gomez

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Mai tsaron bayan Liverpool, Joe Gomez ya saka hannu kan kwantiragin kaka biyar, domin ya ci gaba da taka leda a kungiyar.

Mai shekara 25, wanda ya koma Anfield a 2015, zai ci gaba da taka leda a Anfield har karshen kakar 2027.

Gomez ya yi wa Liverpool wasa 142, sai dai yana fama da jinyar rauni a gwiwar kafa da idon sawu.

''Har yanzu da kuruciya ta, kuma ina da rawar da zan taka a gaba. Har yanzu da akwai abubuwan da nake koya,'' in ji Gomez.

''Ina da damar nuna kaina a kungiyar nan, bayan gudunmuwa da nake samu daga kociyoyina da wadanda muke taka leda tare, ina da tabbaci cewar zan kara kwazo matuka.''

Wanda ya fara taka leda a matasan kungiyar Charlton Athletic ya taimakawa Liverpool ta lashe Champions League da Premier League da FA Cup.

Haka kuma ya dauki Carabao Cup da Uefa Super Cup da kuma Fifa Club World Cup da yin wasa 21 a kakar da ta wuce.