Mai kyautar kayan marmari da masu tsinkar fure cikin hotunan Afirka

Mai kyautar kayan marmari

Asalin hoton, AKINTUNDE AKINLEYE / REUTERS

Bayanan hoto, Wata Mata ta kai kyautar kayan marmari Osun-Osogbo da ke garin Osogbo a Kudu maso Yammacin Najeriya ranar Juma'a.
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2
masu koyon rawa

Asalin hoton, GORDWIN ODHIAMBO / AFP

Bayanan hoto, Masu koyon rawa na gwaji gabanin bukin da za a gudanar a Kibera da ke ƙasar Kenya ranar Laraba.
Mai zane

Asalin hoton, BILLEL BENSALEM / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A ranar Juma'a wani mai zane yayin da yake zana taswirar Imane Khelif a garin Tiaret da ke kudu maso yammacin Algeria.
Dan rawar Simb

Asalin hoton, RICCI SHRYOCK / AFP

Bayanan hoto, A ranar Litinin wani ɗan rawar Simb ya yi wa fuskarsa fenti tare da sanya kayan gargajiya a Dakar babban birnin ƙasar Senegal.
Dan rawar Simb

Asalin hoton, RICCI SHRYOCK / AFP

Bayanan hoto, ƙungiyar na wasanni a lokuta da dama cikin shekara har da lokacin gasar kokawa da kuma ranar samun ƴancin-kai.
Masu halartar biki

Asalin hoton, AKINTUNDE AKINLEYE / REUTERS

Bayanan hoto, Mutane da dama ne ke halartar bikin na Osun a kowace shekara.
Masu wasan takobi

Asalin hoton, EMMANUEL CROSET / AFP

Bayanan hoto, Kashegari an gudanar da wasannin takobi a birnin Johannesburg da ke Afrika ta Kudu.
Dan wasan Boswana

Asalin hoton, MONIRUL BHUIYAN / AFP

Bayanan hoto, Dandazon mutane na gaishe da Letsile Tebogo ranar Talata a Gaborone bayan ɗan ƙasar ta Botswana ya samu lambar zinare ta wanda ya fi kowa gudu a duniya a tseren mita 200 a wasannin Olympics.
Masu zanag-zanga

Asalin hoton, SALVATORE DI NOLFI/EPA

Bayanan hoto, Yayin da aka koma tattaunawar tsagaita wuta ranar Laraba, masu zanga-zangar rikicin Sudan a ƙasar Switzerland sun buƙaci a kawo ƙarshen yaƙin a ƙasarsu
Masu tsinko fure

Asalin hoton, AHMED GAMAL / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Ranar Lahadi a Masar ma'aikata sun tsinko furannin Jasmine a kusa da Kogin Nilu.
Mai haska na'ura

Asalin hoton, AHMED MOSAAD / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A ranar ne kuma wani mutum ya haska wata na'ura sararin sama cikin dare a gaban 'yan kallo.