Al'ummar Katsina sun yi sulhu da Ado Aleru da wasu manyan yanfashin daji

Asalin hoton, Twitter
Wasu al'ummar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya sun yi sulhu da wasu shugabannin ƴanbindiga da suka addabe su.
Al'ummar garin Bicci da ke yankin ƙaramar hukumar Danmusa sun zauna tare da Ado Aleru da sauran wasu shugabannin 'yanbindigan akalla goma, kamar yadda kwamishinan tsaro da harakokin cikin gida na jihar Katsina Dakta Nasiru Mu'azu ya shaida wa BBC.
"An zauna da Ado Aleru da Kamilu Buzaru da Dogo Nahali da Wada Jargaba da Dahiru Buzu haka ma da Nagoggo," in ji shi.
Ya ƙara da cewa, a ɓangaren al'umma akwai limamai da ƴankasuwa da shugaban ƙaramar hukumar Danmusa.
"Ƴanbindigar ne suka zo suka nemi zaman lafiya, don haka ne aka háɗu aka tattauna domin tabbatar da zaman lafiyar," in kwamishinan tsaron na Katsina.
Na yi sulhun ne dai duk da cewa gwamnatin Katsina ta sha nanata cewa ba za ta yi sulhu ko sasanci da ƴanbindiga ba, amma kwamishinan tsaron Nasiru Muazu ya ce buƙata ce daga ɓangaren ƴanbindigar don haka gwamnati ta ba su dama.
Ya ce ƴanbindigan sun bayar da tabbacin ajiye makamansu tare da sako wasu mutane da suka yi garkuwa da su.

Asalin hoton, Twitter
A baya dai an yi irin wannan zama da wasu shugabannin ƴanbindiga da suka addabi yankunan kananan hukumomin Jibia da Batsari, inda aka samu sauƙin hare-haren.
Wannan na zuwa a yayin da rundunar ƴansandan jihar Katsina ta ce ta ceto mutum 73 da aka yi garkuwa da su.
Ta kuma ce ta kama mutum 75 waɗanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban a faɗin jihar.
Sadiq ya ce makaman da aka ƙwato daga wajen mutanen sun haɗa da bindigar AK-49, karamar bindiga ƙirar pistol, ɗaruruwan harsasai, babura biyu da kuma shanu 174 da ake zargin sun sace.
Ya ce ana ci gaba da kula da waɗanda aka kuɓutar daga hannun masu garkuwan.











