Muhimman abubuwa 10 da Tinubu ya faɗa a jawabinsa na cika shekara biyu

Tinubu

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi wasu maganganu masu ɗaukar hankali a cikin jawabinsa da ya yi wa ƴan Najeriya, albarkacin cikar sa shekaru biyu cif-cif da kama aiki.

A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne aka rantsar da Bola Tinubu a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar na 16.

BBC ta yi nazari dangane da jawabin nasa ga kuma wasu maganganu masu jan hankali da ta naƙalto muku.

'Dole ce ta sa na cire tallafin man fetur'

Shugaba Tinubu ya ce dole ce ta sa shi cire tallafin man fetur da rage darajar naira saboda yanayin da "na gada na buƙatar sauya akalar ƙasar. Kuma hakan ne ya sa ba tare da ɓata lokaci ba na ƙaddamar da wasu tsare-tsare guda biyu".

Tinubu ya ce hakan ne ya sa ya cire tallafin mai da aka kwashe shekaru ana ta faman magana a kansa wanda ke amfana wa wasu tsirari. Sannan kuma "na fito da tsarin rufe hanyar rashawa mai alaƙa da musayar kuɗaɗen ƙasar waje."

Sauya Najeriya - "Renewed Hope"

Shugaba Tinubu ya ce ta hanyar ajandarsa da ake kira "Renewed Hope" wani shiri na sabunta Najeriya, ya ce gwamnatinsa ta samu nasarar shawo kan rashin daidaton tattalin arziƙin ƙasar da inganta sha'anin tsaro a faɗin ƙasar da rage rashawa da cin hanci da kuma fitar da ɗumbin al'ummar ƙasar daga talauci.

'Farashin kaya na saukowa'

A jawabin nasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce farashin kaya a ƙasar ya fara faɗowa inda farashin shinkafa da sauran nau'in abinci ya fara sauka.

'Mun rage bashin da ake bin mu'

Shugaba Tinubu ya ce "matsayinmu a fagen bashi da rance na inganta. Abin da muke biya bashi da kuɗaɗen shigar da muke samu ya faɗo da kaso kusan 100 idan aka kwatanta da shekarar 2022 zuwa ƙasa da kaso 40 a 2024."

Ya ƙara da cewa "mun biya duk abin da ake bin mu sannan mun ƙara yawan kuɗin asusunmu na ƙasar waje da kusan kaso 500 daga dala biliyan huɗu a 2023 zuwa biliyan 23 a ƙarshen 2024."

To sai dai kuma shugaban bai yi magana ba dangane da sukar da ake yi wa gwamnatin nasa dangane da ciyo bashin da ke neman kai wa naira tiriliyan fiye da 180.

'An yi wa mata 4,000 tiyatar haihuwa kyauta'

Asibiti

Asalin hoton, Others

Bisa abin da ya shafi sha'anin lafiya, shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa a cikin shekarun biyun da ya kwashe yana mulki, "tana farfaɗo da cibiyoyin kula da lafiya matakin farko guda 1,000 a faɗin ƙasar. Sannan kuma za a ɗaga likkafar ƙarin 5,500 a ƙarƙashin shirinmu na "Renewed Hope"."

"Muna kafa cibiyoyin kula da masu cutar daji guda shida. An kammala guda uku. Muna yi wa al'umma wankin ƙoda akan kuɗi kaɗan. Sannan kuma ƙarƙashin shirin shugaban ƙasa na inganta lafiyar mata masu ciki, an yi wa mata fiye da 4,000 tiyatar haihuwa a kyauta. Sannan mun faɗaɗa shirin inshorar lafiya daga mutum miliyan 16 zuwa 20 a shekaru biyu." In ji Shugaba Tinubu.

'Mun kori masu garkuwa da mutane'

Tsaro

Asalin hoton, Getty Images

Dangane da abin da ya shafi fannin tsaro, Bola Tinubu ya ce an samu gagarumar nasara a harkar tsaro tun bayan hawansa mulki shekaru biyu da suka gabata.

"Tun hawana kan mulki, gwamnatinmu ta inganta aiki tare tsakanin jami'an tsaro da kuma inganta walwalarsu."

"A wasu yankunan arewa maso yammaci da muka samu na ƙarƙashin masu garkuwa da jama'a, yanzu sojojinmu sun dawo da doka da oda. Manoma na komawa gonakinsu. Jama'a na bin hanyoy zuwa garuruwansu. Jami'an tsaronmu na ceto jama'ar da aka yi garkuwa da su." In ji Tinubu.

'Mun samar da tarakta ga manoma'

Noma

Asalin hoton, Getty Images

Shugaba Tinubu ya ce ɗaya daga cikin manyan sauye-sauye da gwamnatinsa ta samar ta hanyar shirinsa na "Renewed Hope" shi ne inganta sha'anin noma.

"Mun ƙaddamar da shirye-shiryen da suka bunƙasa hanyoyin samar da abinci a cikin gida, da ƙarfafa wa manoma gwiwa da tabbatar da farashin abinci ya daidata. Mun kuma zuba kuɗi a harkar noman zamani ta hanyar samar da dubban motocin tirakta da sauran kayan noma da kuma taki.

'Mun inganta lantarki'

A jawabin nasa na cika shekara biyu da kama aiki, Shugaba Bola Tinubu ya ce sun samar da hanyoyin samun makamashi maras ɓata muhalli.

"Mun ƙaddamar da shirin inganta samar da wutar lantarki ta hanyar ɗaga likkafar samar da wutar da inganta hanyoyin raba ta da sanya kuɗaɗe wajen samar da wutar ta hanyar hasken rana domin bai wa gidajenmu da masana'antu da kasuwannin da makarantu da asibitoci wutar lantarki." In ji Tinubu.

'Lokacin yafe wa mutane haraji ya wuce'

Dangane da batun haraji kuma, shugaban Tinubun ya ce ɗaya daga cikin manyan nasarorin da suka shi ne matakin jarumta da suka ɗauka dangane da tsarin yi wa haraji kwaskwarima wanda "tuni yake samar da alkairi".

"Zuwa ƙarshen 2024, harajinmu da kuɗin shigarmu sun ɗaga daga kashi 10 zuwa 13 a cikin shekara guda".

Shugaban ya kuma ce "lokacin yafe wa mutane haraji ya wuce. A saboda haka muka fito da tsare-tsaren da za su inganta ƙere-ƙere, da fasaha da noma da kuma inganta tattalin arziƙi." In ji Tinubu.

'Mun gyara da gina manyan tituna'

Tituna

Asalin hoton, Getty Images

Daga ƙarshe, shugaba Tinubu ya jadda ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da samar da kayan more rayuwa cikin har da tituna.

"Ƙarƙashin shirin "Renewed Hope" gwamnatin tarayya na ci gaba da ayyukan ginawa da gyara manyan hanyoyi a shiyyoin ƙasar baki ɗaya."

Titunan da shugaban ya lissafa a jawabin nasa su ne na Abuja-Kaduna-Zaria-Kano da na Mile-Oturkpo-Makurdi da titin Legas-Calabar da na Abuja-Lokoja-Benin.

Sauran su ne titin Enugu-Onitsa da na Oyo-Ogbomosho da na Sokoto-Badagry. Sai kuma Enugu-Port Harcourt da kuma titin da zai haɗa babbar gadar Second Naija bridge zuwa yankin Bodo-Bonny.