Yadda wasu ƴan Afirka ke ƙoƙarin kafa ƙasarsu a Scotland, ƙarfi da yaji

Mutanen uku sun kwashe makonni suna zama a dajin, inda suka matsa kaɗan daga filin da aka kore su

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Mutanen uku sun kwashe makonni suna zama a dajin, inda suka matsa kaɗan daga filin da aka kore su
    • Marubuci, James Cheyne
    • Aiko rahoto daga, Jedburgh
    • Marubuci, Rachel Grant
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Wasu ƴan Afirka da aka kora daga gonar wasu turawa a kan iyakar ƙasar Scotland - sun matsa gaba kaɗan inda suka sake yin sansani a wani fili mai nisan ƴan motoci.

Wasu jami'an ƴansanda biyar sun shiga sansanin nasu a cikin wani daji kusa da garin Jedburgh da safe, lokacin da mutanen uku ke bacci.

Mutanen na iƙirarin kafa wata ƙasa da suke kira Masarautar Kubala.

Mutanen sun sake kwashe kayansu tare da matsawa wani wuri gaba kaɗan, kusa da katangar kan iyaka.

"Ƙabilar" tana zama a dajin ne na tsawon makonni duk da ƙoƙarin da hukumomi suka yi na korar su daga yankin.

Mataimakin shugaban hukumar kula da lamurran al'umma ta yankin Scotland, Scott Hamilton, ya ce yanzu haka hukumomi na ƙoƙarin gano wanda ya mallaki filin da mutanen suka yi sansani a ciki.

Ya ce: "Muna tantance matsayarsu a bisa doka.

"Kamar suna zaune ne a fili mallakin wani, amma yana iya yiwuwa kuma dajin gwamnati ne.

"Muna ƙoƙarin tantance hakan, daga nan sai mu ɗauki mataki."

A makon da ya gabata ne ofishin tabbatar da doka na Sheriff Peter Paterson ya miƙa wa mutanen takardar umarnin tashi daga dajin da suka yi sansani.

Mutanen sun yi iƙirarin cewa suna so ne su sake karɓo filin da aka ƙwace daga hannun kakannin-kakanninsu shekaru 400 da suka gabata - sai dai hukumomi sun ce suna karya doka.

Mutanen na ci gaba da jan hankalin mutane a shafukan intanet, inda sama da mutum 100,000 ke bibiyar su a shafukan TikTok da kuma Facebook, sannan labarinsu na ƙara karaɗe duniya.

Kofi Offeh ɗauke da baƙar leda da kuma wata jar jaka. A gefensa kuma wata rumfar wucin gadi ce da sauran kayayyaki.

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Kofi Offeh, wanda ke kiran kansa Sarki Atehehe, ɗan asalin ƙasar Ghana ne
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ɗan asalin ƙasar Ghana Kofi Affeh mai shekara 36, da Jean Gasho mai shekara 42 daga Zimbabwe sun isa yankin garin Jedburgh mai yawan tsaunuka ne a lokacin bazara.

Suna yi wa kansu laƙabi da Sarki Atehe da Sarauniya Nandi, inda suka yi sansani a wani tudu da ke gefen garin, kusan da kan iyakar yankin na Scotland.

Daga baya sai wata mata mai suna Kaura Taylor daga jihar Texas ta Amurka ta isa wurin nasu, inda ta laƙaba wa kanta suna Asnat.

A ranar Talatar makon da ya gabata ne jami'an ofishin tabbatar da doka tare da taimakon jami'an ƴansanda huɗu suka fitar da mutanen daga filin da suka fara zama.

An ji yadda mutanen suka riƙa yin ihu da ƙarfi a lokacin da ake ƙoƙarin korar su daga wurin.

Jami'ai su tsaya a wurin na tsawon awa ɗaya da rabi kafin kammala warware bukkokin da suka kafa da kuma tattara komatsansu.

Daga nan ne mutanen suka tsallaka shingen waya ta ɗaya gefen suka sake kafa wani sansani.

Mutanen sun ƙi cewa komai a lokacin da BBC ta tambaye su abin da ya faru.

An shanya rumfunan wucin gadi a kan wani shingen waya, bayan rushewarsu.
Bayanan hoto, Tun farko mutanen sun yi sansani ne a wani fili da ke tsallaken wani shingen waya

Mutanen suna ikirarin cewa kakannin-kakanninsu ne suka mallaki filin, inda a yanzu suke ikirarin kafa Daular Kubala.

Tun a watan Yuli ne hukumomin Scotland suka fara tayar da su daga wuri na farko da suka yi sansani.

Tun farko Mista Offeh ya ce "ba ya jin tsoron" duk wani umarni na tayar da su fdaga dajin.

Waɗanda suka mallaki filin, David da Mary Palmer, sun yi nasara a ƙorafin da suka shigar na neman a kori mutanen daga filin.

Taswirar wurin da mutanen suka yi sansani kusa da garin Jedburgh a yankin Scotland
Bayanan hoto, Taswirar wurin da mutanen suka yi sansani kusa da garin Jedburgh a yankin Scotland

A makon da ya gabata, jami'in tabbatar da doka Mista Hamilton ya bayyana mutanen a matsayin masu karya doka bayan yin sansani a fili mallakin wasu mutane.

Ya ce abin da suka yi ya tursasa wa mai filin ɗaukar matakin neman ɗaukin hukuma.

Ya bayyana cewa abin damuwa ne yadda mutanen suka bijire wa umarnin hukuma na ficewa daga filin a cikin wa'adin da aka ɗeba musu.

Ya ce: "Sun ƙi bayar da duk wata damar tattaunawa da hukumomi.

"Za mu iya taimaka musu, amma ba za mu zauna mu sanya musu ido su karya doka ba," in ji shi.

Bayanan bidiyo, Kalli yadda mutanen ke rayuwa a cikin daji da kuma abin da Sarkin nasu ya ce kan umarnin da aka ba su na tashi daga filin