An gano 'fatalwar' mutanen da a Afirka Ta Yamma

Stages in human evolution, illustration

Asalin hoton, Science Photo Library

Bayanan hoto, Labarin sauyin da aka samu a halittar dan adam na kara rikitarwa
An wallafa

An gano wata 'fatalwar' mutanen da da ke zaune a yammacin Afirka, a cewar wasu masana.

Masu binciken sun gano cewa kwayar halittar mutanen ta kunshi kashi biyu zuwa kashi 19 na asalin 'yan kasashen Afirka ta Yamma.

Sun yi amannar cewa hakan ya faru ne kimanin shekara 43,000 da suka gabata.

Masana kimiyya sun alakanta su da mutanen Mende na Saliyo da kuma Yarabawa a Najeriya da kuma kabilar Esan a yammacin Gambia.

An wallafa sabon binciken ne a mujallar Science Advances a wannan mako.

Binciken ya ce mutanen da a Afirka ta yamma sun yi cudanya da wasu mutanen daga wasu wuraren, yadda Turawan da suka yi cudanya da dangin Neanderthal da al'ummar kasashen da ke makwabtaka da ruwa tare da mutanen da daga yankin Asiya wato Denisovans.

Binciken ya yi karin haske kan yadda mutanen da dangin hominins ke kara bambancin kwayoyin halittar 'yan Afirka na yanzu, wanda ba a fahimta sosai ba, duk da cewa Afirka yanki ne mafi yawan al'adu.

Shekaru da dama da suka gabata akwai dangogin mutanen da daban-daban da suka hada da mutanen yanzu da 'yan Neanderthal da kuma na Denisovan.

Da alamu 'fatalwar' mutanen da din ta rabu da wadannan rukuni.

Sriram Sankararaman - wanda ya jagoranci binciken a Jami'ar California da ke Los Angeles - ya shaida wa BBC Newsday cewa ya yi imanin za a samu karin irin wadannan rukunin a nan gaba.

"Yayin da muke samun karin bayani daga al'umomi daban-daban - da kuma ingantattun bayanai - damarmu ta tace bayanan tare da hako wadannan fatalwoyin zai inganta," a cewarsa.