Waiwaye: Mutuwar Sheikh Idris Dutsen Tanshi da sauke Mele Kyari daga shugabancin NNPCL

Sheikh Idris Dutsen Tanshi

Asalin hoton, Dusten Tanshi Majlis/Facebook

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Wannan maƙala ce da ke kawo muku bitar muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi

Sheikh Idris Dutsen Tanshi ya rasu

Sheikh Dutsen Tanshi

Asalin hoton, other

A ranar Juma'ar ƙarshen makon ne kuma aka wayi gari da rasuwar fitaccen malamin addinin musulunci na Najeriya, Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi, wanda ya rasu ranar Alhamis da daddare.

Malamin mai shekara 68 ya rasu ne bayan fama da jinya, inda har ya je neman lafiya ƙasashen Indiya da Saudiyya.

Sheikh Tanshi ya rasu ya bar mahaifiyarsa da mata guda uku da kuma ƴaƴa 32.

Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi ya rasu

Galadiman Kano

A ranar Talata da daddare ne Allah ya yi wa Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi rasuwa yana da shekara 92.

Kafin rasuwarsa, Alhaji Abbas Sanusi ya kasance babban ɗan majalisar Sarki a lokacin marigayi Sarki Ado Bayero a matsayin Wamban Kano da Sarki Aminu Ado Bayero na 15.

Sarkin Muhammadu Sanusi I ne ya fara naɗa shi sarautar sarkin Dawakin tsakar gida hakimin Ungogo a 1959, sannan a 1963 kuma Sarkin Kano Inuwa ya yi ɗaga likkafarsa zuwa Dan Iya.

Marigayin ya zama babban ɗanmajalisar Sarki a 1987 kuma hakimin Nasarawa.

Tinubu ya cire Mele Kyari daga shugabancin NNPCL

Tsohon shugaban NNPCL

Asalin hoton, NNPCL/X

A tsakiyar makon ne kuma shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya cire Mele Kyari daga shugabancin kamfanin mai na ƙasar na NNPCL, inda ya maye gurbinsa da Injiniya Bashir Bayo Ojulari.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaba Tinubun, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X, ya ce hakan ya faru ne sakamakon wani garambawul da shugaban ya yi wa kamfanin.

Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya rushe hukumar gudanarwar kamfanin ƙarƙashin shugabancin Cif Pius Akinyelure da kuma Mele Kyari wanda shi ne shugaban kamfanin.

"Shugaba Tinubu ya rushe dukkan mambobin hukumar da aka naɗa ƙarƙashin Pius Akinyelure da Mele Kyari a 2023." In ji sanarwar.

Tinubu ya tafi ziyarar aiki Faransa

Bola Tinubu

Asalin hoton, Bayo Onanuga/X

A ranar Larabar makon ne kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bar Najeriya zuwa ƙasar Faransa domin ziyarar aiki ta mako biyu.

Haka na ƙunshe ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mataimaki na musamman ga shugaban ƙasar kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga.

Shugaban ya ce zai yi amfani da lokacin ziyarar don yin nazari kan yadda gwamnatinsa ta kasance a yayin da ta ke gab da cika rabin zango.

Haka kuma zai duba manyan nasarorin da gwamnatin ta samu tare da duba garonbawul ɗin da ya yi da gaggauta ci gaban da ya ke so a samu a shekara da ke tafe.

Ƴan bindiga sun saki tsohon shugaban NYSC Janar Tsiga

Birgediya Janar Tsiga

Asalin hoton, family

Haka ma a cikin makon ne dai tsohon shugaban Hukumar yi wa Ƙasa Hidima ta Najeriya, NYSC, Birgediya Janar Mahrazu Tsiga, mai ritaya da ƴan bindiga suka yi garkuwa da shi, ya samu kuɓuta.

Janar Tsiga ya shafe kwana 56 a hannun ƴan bindigar, kafin su sake shi.

An dai yi garkuwa da shi ne ranar 5 ga watan Fabrairu, a garin mahaifarsa ta Tsiga da ke karamar hukumar Bakori na jihar Katsina - tare da wasu mutum 13.

Duk da cewa ƙaramar hukumar Bakori na fama da matsalar 'yanbindiga, amma garin Tsiga bai saba fuskantar irin wannan matsala ba sai a baya-bayan nan.

Jamb ta saka ranar fara jarrabawar wannan shekara

Jamb

Asalin hoton, Jamb/Facebook

A cikin mako ne kuma hukumar shirya jarabawar shiga jami'o'i ta Najeriya, JAMB ta sanar da ranar 25 ga watan Afrilun da muke ciki a matsayin ranar fara jarrabawar wannan shekara ta 2025.

Cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Dakta Fabian Benjamin ya fitar, ya ce za a fara jarrabawar Jamb ta gwaji (Jamb-Mock) a ranar 10 ga watan na Afrilu.

Hukumar ta kuma buƙaci masu rubuta jarrabawar su fitar da katunan jarrabawar da ake kira 'Exam Slip' - waɗanda suka ƙunshi cikakkun bayanan ranar da mutum zai yi jarrabawar da lokaci da kuma wurin da zai yi ta.

''Ana buƙatar masu rubuta jarrabawar su fara fitar da katunan tun daga ranar 3 ga watan Afrilu, domin samun isasshen lokacin shirya wa jarrabawar'', in ji sanarwar.