Arsenal ta barar da damar karshe ta lashe Premier na bana

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta yi rashin nasara a Emirates da ci 3-0 a hannun Brighton a wasan mako na 36 a gasar Premier League ranar Lahadi.
Brighton ta fara cin kwallo bayan da aka koma zagaye na biyu ta hannun Julio Enciso, sannan Deniz Undav ya zura na biyu saura minti hudu a tashi wasan.
Daf da alkalin wasa zai tashi karawar Pervis Estupinan ya ci wa Brighton kwallo na uku, kenan ta hada maki ukun da take bukata.
Da wannan sakamakon Brighton mai kwantan wasa biyu ta hada maki 58 tana ta shida a teburin Premier League.
Arsenal kuwa tana mataki na biyu da tazarar maki hudu tsakaninta da Manchester City mai kwantan wasa, wadda ke neman maki uku nan gaba ta lashe kofin bana.
Saura wasa biyu ya rage wa Arsenal, kuma idan ta ci dukka za ta hada 87, bayan da tuni City keda 85, wadda za ta kara da Chelsea a Etihad, sannan ta je Brighton, sai Brentford ta karbi bakuncin City.
Wasannin da ke gaban Arsenal guda biyu:
Premier League Asabar 20 ga watan Mayu
- Nottingham Forest da Arsenal
Premier League Lahadi 28 ga watan Mayu
- Arsenal da Wolves
Karawar da suka rage wa Brighton:
Premier League Alhamis 18 ga watan Mayu
- Newcastle da Brighton
Premier League Lahadi 21 ga watan Mayu
- Brighton da Southampton
Premier League Laraba 24 ga watan Mayu
- Brighton da Man City
Premier League Lahadi 28 ga watan Mayu
- Aston Villa da Brighton
An zura kwallo 25 a ragar Arsenal a Premier League a gida a kakar, karon farko tun bayan da aka dura mata 24 a 2019/20 tun bayan da ta koma Emirates.










