Postecoglou ya gyara Tottenham cikin ƙanƙanin lokaci - Guardiola

gh

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce kocin Tottenham Ange Postecoglou “ya ƙara kyautata kwallon kafa”.

Kungiyoyin biyu za su fafata da junansu a ranar Lahadi, yayin da maki uku ne kawai ya bambanta City da take matsayi na biyu da Tottenham da ke matsayi na huɗu.

Postecoglou ya karɓi Spurs a watan Yuni kuma sai da suka buga wasa 10 a wannan kakar ba tare da an yi nasara a kansu ba, amma sun yi rashin nasara a wasanninsu uku na ƙarshe.

“Cikin ‘yan watanni ka duba yadda ya sauya ƙungiyar,” in ji Guardiola.

“Ya yi kyau da ƙungiyar cikin ƙanƙanin lokaci. Dole ka yaba masa har a wasannin da yake nasara a ƙarshen lokaci. Ina jin daɗin yadda suke abubuwa da dama – dama nawa suke samu da kuma yadda suke buga wasa cikin yunwar samun maki.”

Guardiola ya ce yana sha’awar ƙwarin gwiwar Postecoglou da kuma salon wasan ƙungiyarsa na burge shi.

“Ina ganin dukkan magoya bayan ƙungiyar da mutanen Ingila na farin cikin tasirinsa a ƙungiyar,” in ji Guardiola.

Gabanin ya koma Spurs, Postocglou ya jagoranci Celtic inda ya lashe gasar Premier Scottland biyu a kaka biyu, sannan ya taimaka wa ƙungiyar Yokohama F ta kawo ƙarshen shekara 15 ba tare da cin lig ɗin Japan ba a 2019.