United na sa ran Ronaldo zai ci gaba da zama a Old Trafford, Chelsea na bukata

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United na sa ran Cristiano Ronaldo zai kasance cikin 'yan wasanta a kakar da za a fara ta bana, duk da wasu rahotanni da ke cewar Chelsea za ta yi zawarcinsa.
Wakilin Ronaldo, Jorge Mendes ya gana da sabon shugaban Chelsea, Todd Boehly a makon jiya, kuma an ce zance dan kwallon tawagar Portugal suka yi.
Wata majiya daga United ta sanar da cewar Mendes, yana da 'yan wasa da yawa da yake wakilta, da kyar ne idan batun cinikin Ronaldo suka tattauna.
United ta kara tabbatar da cewar ba za ta sayar da Ronaldo, mai shekara 37 ba.
Zakaran Ballon d'Or karo biyar yana da sauran yarjejeniyar kaka daya a Old Trafford, kuma sabon koci, Erik ten Hag zai yi amfani da shi a kakar da za a fara a farkon makon Agusta.
Ronaldo yana daga kadan daga cikin 'yan wasan United da ba a cika suka ba daga magoya baya a kakar da ta wuce.
Ronaldo shi ne na uku a jerin wadanda suka ci kwallo da yawa a Premier League da aka karkare, wadda Manchester City ta lashe.
Sai dai kuma wasu na sukar Ronaldo cewar rashin sa matsi a wasu wasannin da yake, shi ne ya sa United ba ta taka rawar da ta kamata.










