Man City na nazari kan Pogba, Ƙungiyoyin Firimiya na rububin Kudus

Pogba

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester City na nazari kan dauko ɗan wasan tsakiya a Faransa, Paul Pogba, wanda ke iya komawa wasa daga watan Maris bayan haramci wasa da aka kakaba ma sa kan ta'amali da kwayoyin kuzari. Sai dai tsohon ɗan wasan na Manchester United da Juventus bai wani damu kan yi ma ta wasa ba. (Independent)

Newcastle United na kalubalantar Arsenal da Liverpool a cinikin ɗan wasan gefe a West Ham, Mohammed Kudus mai shekara 24, amma dole sai ƙungiyar ta sayar da ɗan wasa a cikin watan Janairu domin samun kuɗin sayen ɗan wasan na Ghana. (Mirror)

Ɗan wasan baya a Liverpool da Ingila, Trent Alexander-Arnold mai shekara 26 babu wata yarjejeniya a hannusa kuma ya ce ba zai cimma sabuwar kwantiragi da kungiyarsa ba. (Sky Sports)

Alexander-Arnold ya kasance wanda Reald Madrid ke hari, sannan kungiyar na kuma son dauko ɗan wasan tsakiya da tsawaita zaman mai tsaron ragar Thibaut Courtois, mai shekara 32. (Fabrizio Romano via Teamtalk)

Kocin Manchester United, Ruben Amorim na farautar ɗan wasan baya da tsakiya a watan Janairu. (Football Insider).

Bayern Munich ba ta da niyyar maye gurbin ɗan wasanta na Ingila, Harry Kane da ya samu rauni a cewar daraktan wasannin ƙungiyar ta Jamus, Max Eberl. (Sky Sports Germany)

Ɗan wasan Ingila Anthony Gordon ya yi watsi da raɗe-raɗin cewa ya so barin Newcastle, kafin maganar tafiya Liverpool ta taso. (Sky Sports)

Manchester City na son dauko ɗan wasan Netherlands, Jeremie Frimpong, mai shekara 24 daga Bayer Leverkusen. (Football Insider)

Wolves da Nottingham Forest ke kan gaba a farautar ɗan wasan Atalanta Ben Godfrey, mai shekara 26 (Sun)

AC Milan na iya sayar da ɗan wasanta na FaransaTheo Hernandez, mai shekara 27, a watan Janairu (Gazzetta dello Sport - in Italian)