An dakatar da wasan Bundesliga bayan da aka jefi mai tsaron raga

Patrick Drewes

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

An dakatar da wasan Union Berlin a gida a Bundesliga da Bochum kusan sama da rabin awa, bayan daga cikin ƴan kallo aka jefi golan baƙi, Patrick Drewes.

Mai shekara 31, na shirin buga tamaula jim kaɗan a komawa zagaye na biyu ana cin 1-1, sai aka jefi golan da wani abin da ake gani kamar da abin kunna sigari.

Daga nan Drewes ya durkusa gwiwarsa biyu kasa, saboda haka sai aka dakatar da wasan, inda likitoci suka duba lafiyarsa.

Daga nan alkalin wasa Martin Petersen ya dakatar da karawar, sannan ya bukaci ƴan wasa da su koma ɗakin hutu da ake canja kaya.

Ɗan wasan Bochum ɗan kasar Japan, Koji Miyoshi ya karɓi jan kati a minti na 13 da take leda, daga baya ƙungiyar ta zura ƙwallo a raga ta hannun Ibrahima Sissoko.

Sai da wasan ya yi nisa ne Benedict Hollerbach na Union Berlin ya farke ƙwallo, amma haka aka tashi daga karawar.

Bochum ta ci gaba da yin wasa ba tare da nasara ba, bayan fafatawa 14 da maki tara, ita kuwa Union Berlin tana ta 12 teburi da maki 17.