Arsenal da Man United na zawarcin Chiesa, Leverkusen za ta ɗauki Matip

Joel Matip

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Bayer Leverkusen na neman ɗaukar tsohon ɗan bayan Liverpool da Kamaru, mai shekara 32 , Joel Matip bayan kwangilarsa ta ƙare a bana. (Sky Germany)

Ɗan bayan Ingila Joe Gomez ya ce ba shi da niyyar barin Liverpool a bana, duk da cewa ƙungiyar na shirin miƙa shi ga Newcastle domin amso ɗan wasan gefen Ingila da Newcastle mai shekara 23, Anthony Gordon, 23. (Mirror)

Chelsea za ta shiga zawarcin ɗan wasan tsakiyar Celtics mai shekara 23 Matt O'Riley, idan ɗan wasan tsakiyar Ingila mai shekara 24, Conor Gallagher, ya ba rta zuwa Atletico Madrid. (Sky Sports)

Borussia Dortmund ta shige gaban Chelsea da Aston Villa a zawarcin ɗan wasan gaban Hoffenheim mai shekara 21, kuma ɗan ƙasar Jamus, Maximilian Beier. (Sky Germany)

AC Milan ta gabatar da tayin £12.78m domin sayen ɗan bayan Brazil mai shekara 25, Emerson Royal, daga Tottenham. (Fabrizio Romano)

Ɗan wasan gaban Jamus mai shekara 31, Niclas Fullkrug, ya tsallake gwajin lafiya a West Ham, gabanin komawar sa ƙungiyar daga Borussia Dortmund. (Sky Sports)

Leeds United ta shirya ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Ingila mai shekara 19, Bobby Clark daga Liverpool. (Football Insider)

Juventus na shirin cefanar da ƴan wasanta takwas, ciki harda ɗan wasan gaban Italiya mai shekara 26, Federico Chiesa, wanda ake alaƙantawa da komawa taka leda a Tottenham. (Mail)

Manchester United da Arsenal sun shiga zawarcin Chiesa, wanda ya shiga shekarar ƙarshe ta kwangilarsa a Tottenham kuma ake sa ran farashinsa zai faɗi. (Teamtalk)

Everton na fuskatar matsin lamba domin ganin ta sayar da ɗan wasanta na baya mai shekara 22 kuma ɗan Ingila, Jarrad Branthwaite, ƙasa da asalin farashinsa. (Football Insider)