Liverpool ta yi watsi da tayin da Southampton ta yi wa Carvalho

Fabio Carvalho

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Liverpool ta ƙi amincewa da tayin da Southampton ta yi na sayen, Fabio Carvalho kan kusan fan miliyan 15.

Southampton ta daɗe tana sha'awar ɗaukar ɗan wasan mai shekara 21, amma tayin da ta yi wa ɗan ƙwallon ya yi kasa da abinda Liverpool za ta sayar da shi.

Carvalho ya taka rawar gani a wasannin sada zumunta da Liverpool ta yi a Amurka, bayan da ya zura kwallo a ragar Arsenal da Manchester United.

Sabon kocin Liverpool, Arne Slot ya yi imanin cewa zai iya amfani da shi a tsarin sa na 4-2-3-1 a bana, sai dai idan aka yi mai tsoka, to Liverpool za ta sayar da shi.

Da yake da yamar ƴan wasan Liverpool na komawa don karbar horo, Slot ya samu damar tantance matasan da ya kamata ya yi amfani da su a kakar nan har da Carvalho da Sepp van den Berg.

To sai dai da kyar ne idan Carvalho zai samu gurbin buga wa Liverpool wasanni yadda ya kamata da zarar Luis Diaz da Darwin Nunez da Cody Gakpo, suka kammala hutu, bayan Copa America da Euro 2024 da suka buga.

Wasu ƙungiyoyin da dama sun nuna sha’awarsu ta neman Carvalho, wanda ya shafe kakar bara a matsayin aro a RB Leipzig da kuma Hull City.

Ya zura kwallo tara a wasa 20 na Hull Ciyu, amma ana tunanin watakila Liverpool ta kara bayar da aronsa.