Ba don kuɗi na koma Chelsea daga Barcelona ba - Marc Guiu

Marc Guiu

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Sabon ɗan wasan Chelsea Marc Guiu ya ce "mafarkinsa" ne ya taka leda a Premier, ya musanta rahotannin cewa ya bar Barcelona don saboda kuɗi ne.

Ɗan wasan mai shekaru 18 ɗan Sifaniya, ya samu damar da zai nuna kansa a wasannin atisaye da Chelsea ke yi a Amurka, wadda ta ɗauko shi daga Barcelona.

Guiu, wanda ya zura kwallo daya a wasa hudu a wasannin da Chelsea ke yi a Amurka, ya ki amincewa da sabon kwantaragi da Barcelona ta gabatar masa kafin ya koma Stamford Bridge.

Ya musanta rahotannin da ake yi a Sifaniya da cewa saboda kuɗi ne ya bar Barcelona ya koma Chelsea da taka leda, amma ya ce: “Ba haka ne ya sa na koma Ingila ba.

"Ko yaushe ina da burin yin wasa a gasar Premier League, kuma Chelsea babbar kungiya ce mai ɗimbin tarihi.

"Yana yi ne mai wahala ka yanke hukunci, amma dama ce mai kyau, don haka dole ne in koma Ingila da tamaula."

An tambayi Guiu ko a shirye yake ya buga gasar Premier ta bana, ko kuma zai fi son zuwa buga wasannin aro, sai ya amsa da cewa: “Na mai da hankali ne kan wasannin atisayen da Chelsea ke yi a Amurka.

"Amma kocin Chelsea Enzo Maresca ya gaya min cewa akwai wani shiri na musamman da ya shafi hazikan matasa ƴan wasa, wanda ina ciki.''

"Ina jin a shirya nake. Muna aiki tuƙuru kowace rana a ciki da wajen filin wasa. Don haka ina ganin a shirye nake in kasance cikin filin wasa, kuma in taimaka wa kungiyar a lokacin da ake bukata ta.”