Gwamnan Gombe bai isa ya yi min ritaya a siyasa ba - Sanata Goje

Asalin hoton, Muhammad Adamu Yayari/FB
Yayin da ake ci gaba da hasashen matakin da zai ɗauka bayan dambarwar da ta taso daga zaɓukan fitar da gwani na jam'iyyar APC, wadda ta kai ga ya sara tikitin takarar sanata, tsohon gwamnan jihar Gombe kuma sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya, Muhammed Ɗanjuma Goje ya ce zai ci gaba da mara wa jam'iyyar APC baya domin ta samu nasara a zaɓe mai zuwa.
A baya dai an yi hasashen cewa jigon a siyasar jihar Gombe da ke yankin Arewa maso gabashin Najeriya zai sauya sheƙa zuwa wata jam'iyya domin ƙalubalantar hana shi takara a APC duk da cewa shi ke kujerar a yanzu haka.
Sai dai a hirar shi da BBC, Sanata Goje ya ce ya ɗauki rashin samun tikitin nasa a APC a matsayin ƙaddarar rayuwa daga Allah, kuma ya gamsu cewa ya cimma duk matakin da ya kamata ya kai a siyasance domin haka lokaci ne ya zo na ''komawa gefe ya bari ƴan baya su shiga.''
''Ai da mu aka kafa jam'iyyar APC, kuma bai kamata mutum ya gina gida ya bar gidan ba,'' in ji Sanata Goje.
Ya ce: ''Na je Gombe na yi bayani wa magoya baya na cewa tun da aka samu tangarɗa wajen tsayawa a jam'iyyata ta APC, na yanke hukuncin ba zan tsaya takara ba.''
Ya yi bayanin cewa shekara 16 kenan yana majalisar dattawan Najeriya, inda ya riƙe muƙamai daban-daban a majalisar domin haka yana ganin ba abin da ya dace ya yi sai godiya ga Allah.
Dangane da ganin da wasu ke yi cewa an ci amanar Sanata Goje saboda rashin ba shi damar tsayawa takara duk da tsayawar da yi kan kafuwar gwamnatin jam'iyyar a matakin ƙasa da kuma jihar Gombe, sanatan ya ce ''ai a matsayin musulmi na san komai daga Allah yake, ba wani maganar cin amana. Ni a siyasa sai dai in nuna godiya.''
Sanata Goje ya ce shi tun a 2019 ya yanke shawarar ba zai sake takarar majalisar dattawa ba, amma daga baya jama'ar da yake wakilta suka tilasta mashi har ya yi takarar kuma ya ci gaba da wakiltar su.
''Wannan karon ma sauri aka yi, ban yi niyyar tsayawa zaɓe ba, amma an matsa mani ne, kuma na tsaya. To tunda Allah ya nufa ba zan tsaya ɗin ba, babu wani damuwa a ciki.
"Kuma ma abin ya zamo, tun ina takarar da sa'oi na, har na dawo ina takara da yara na, ban so in kira sunayen su, amma na yi takara da waɗanda ni na sanya su a siyasa, kuma yanzu wanda aka bai wa takara a PDP kamar jika na ne a siyasa,'' in ji Goje.
Tasiri da makomar siyasar Sanata Goje a Gombe
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sanata Danjuma Goje ya kuma yi tsokaci a kan rahotannin da wasu ke yaɗawa cewa gwamnan Gombe Muhammad Inuwa Yahaya ya yi mashi ritayar siyasa ta la'akari da abin da ya faru, inda ya ce ''Ba Inuwa Yahaya ne ya yi mani ritaya a siyasa ba, Allah ne ya sa ba zan yi wannan al'amari ba.''
Ya ƙara da cewa ''ai kafin Inuwa Yahaya ma na sa Dankwambo, Allah ya ba shi gwamna amma sanadi na, shi ma Inuwa Yahaya Allah ya ba shi gwamna amma sanadi na.''
''Bai isa ya yi mani ritaya ba, kuma bai yi mani ritaya ba, in na ga dama yau, da na ga dama na karɓi tikitin kowacce irin jam'iyya ma, da zan dawo majalisar dattawa.
Kuma ai kwannan nan na je Gombe, kun ga irin taron da aka yi. Da na ce ba zan tsaya takara ba mutane kuka suka yi, akwai waɗanda suka yi 'collapsing' akwai wanda da aka ce ba zan tsaya ba hawan jinin sa ya tashi, wallahi ya rasu,'' in ji Sanata Goje.
Ya jaddada cewa yana da goyon bayan da duk inda ya tsaya zaɓe mutane za su zaɓe shi, amma a matsayin shi na dattijo mai shekara saba'in da wani abu, yana ganin lokaci ya yi da zai koma gefe ya bari wasu su gwada irin tasu haraƙar.
Wane ne Danjuma Goje?
Sanata Mohammed Danjuma Goje fitaccen ɗan siyasar Najeriya ne, wanda a halin yanzu yake wakiltar shiyyar Gombe ta Tsakiya a Majalisar Dattawan Najeriya.
An haife shi ranar 10 ga Oktoba, 1952 a garin Pindiga da ke ƙaramar hukumar Akko a Jihar Gombe. Ya yi karatunsa na digiri a Jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria a fannin Kimiyyar Siyasa.
Goje na ɗaya daga cikin manyan jigajigan siyasar Arewa da ma Najeriya baki ɗaya, inda ya shafe kusan shekaru 45 yana taka rawar gani a fagen siyasa.
Ya fara harkar siyasa tun a Jamhuriya ta Biyu, inda ya zama ɗan majalisar dokoki na jihar Bauchi kafin a fidda jihar Gombe daga baya. Ya riƙe muƙamin Ministan Jiha na Ma'aikatar Wutar Lantarki da Karafa a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Olusegun Obasanjo.
Ya yi gwamnan jihar Gombe har tsawon wa'adi biyu a ƙarƙashin jam'iyyar PDP tsakanin 2003–2011.
Shi ne ya assasa jami'ar jihar ta Gombe, filin jirgin sama na Lawanti, da babban filin wasa na Pantami.
Bayan kammala gwamna, ya tsallaka zuwa Majalisar Dattawa inda yake a wa'adi na huɗu. Ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC, kuma yana ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam'iyyar ta APC.











