Iran ba ta iya biyan albashin mafi yawan jami’an tsaronta - Trump
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi iƙirarin cewa gwamnatin Iran na fuskantar matsalar tattalin arziki har ta kai ga ta kasa biyan albashin mafi yawan jami’an tsaronta.
Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan halin da Iran ke ciki, yana mai zargin gwamnatin ƙasar da kashe masu zanga-zanga a daidai lokacin da take fuskantar matsalar kuɗi.
Ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran “ba ta biyan albashin wani babban ɓangare na sojojinta”, inda ya bayyana lamarin a matsayin babbar matsalar jinƙai da ya kamata a kawo ƙarshenta.
A baya Trump ya ce Iran na cikin “yanayin durƙushewa”, yayin da gwamnatinsa ke ƙara matsin tattalin arziki kan ƙasar.
Zan kawo wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20 - Matawalle
Asalin hoton, Matawalle/X
Ƙaramin Ministan Tsaro na Najeriya, Bello Matawalle, ya ce yana da burin samo wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kuri’u miliyan 20 a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Matawalle ya bayyana hakan ne ranar Talata a Abuja, yayin da dubban magoya bayansa da ’yan jam’iyyar APC suka tarbe shi bayan komawarsa Najeriya.
Ya ce ya shirya fara tattara bayanai da neman kuri’u a faɗin jihohin Najeriya 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja.
“Kamar yadda kuka sani, an fara kamfen, kuma burina shi ne in kawo wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kuri’u miliyan 20 a zaɓen shugaban ƙasa na 2027... Kuma a shirye nake in yi duk abin da zan iya domin tabbatar da mun cimma wannan buri.”
Matawalle ya ce akwai dalilai da dama da suka sa yake ganin ya kamata a sake zaɓar Tinubu a 2027, yana mai cewa shugaban ya yi iya ƙoƙarinsa wajen inganta ayyukan yi ga matasa, tsaro da tattalin arzikin ƙasa a cikin shekaru ukun da ya yi yana mulki.
'Na ga kakana a cikin bidiyon da ƴan bindiga suka fitar a Neja'
Asalin hoton, Umar Muhammad Bago/FB
Waɗanda suka tsira daga wani mummunan hari da ƴanbindiga suka kai a jihar Neja sun shaida wa BBC yadda ƴan bindiga suka kashe mutane da dama tare da yin garkuwa da wasu masu yawa a wasu hare-hare da suka kai a lokaci guda kan yankuna huɗu.
Ƴan bindigar, waɗanda aka ce suna sanye da kayan sojoji, sun kai hare-hare kan ƙauyukan Dekara, Gidan Zana, Sabon Gida da Masaka.
Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya shaida wa BBC cewa an kashe fiye da mutum 40. Sai dai hukumomi sun ce har yanzu ba a tabbatar da haƙiƙanin adadin waɗanda aka kashe ko aka sace ba.
Mazauna yankin na fargabar cewa mutanen da aka yi garkuwa da su na iya zarta adadin da hukumomi suka bayyana.
Wani matashi daga yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya shaida wa BBC cewa mai yiwuwa mutanen da ƴan bindigar suka yi garkuwa da su za su kai kusan 500.
Wannan ƙiyasin ya biyo bayan yaɗuwar wani bidiyo da wata ƴan bindiga suka saki, wanda ya nuna gomman mutane, mata, yara da maza zaune a wani daji.
Matashin ya ce ya gane wasu mutane daga cikin ƴan garinsu a cikin bidiyon.
“Na iya gane mutane da dama. Akwai wani dattijo a cikin bidiyon wanda yake kamar kakana ne. Yana zaune a ƙauyen Gidan Zana,” in ji shi.
Ya ce iyalan mutanen da suka gane ƴan uwansu a cikin bidiyon sun ji daɗin sanin cewa har yanzu suna raye.
Matashin ya ce an binne kusan mutum 30 ranar Litinin, kuma har yanzu ƴan bindigar ba su tuntuɓi mutanen yankin domin neman wani abu na fansar mutanen ba.
Bayanan da BBC ta samu sun nuna cewa mazauna yankuna da dama sun bar gidajensu, inda suka nemi mafaka a wasu jihohin Najeriya da kuma ƙetare iyaka zuwa ƙasar Benin. Wasu daga cikin waɗanda suka tsira kuma na samun kulawa a asibitoci, ciki har da waɗanda suka samu munanan raunuka.
Wani jami’in tsaro ya kuma shaida wa BBC cewa maharan sun dasa bama-bamai a kan hanyoyi, yayin da suke rakiyar mutanen da suka yi garkuwa da su zuwa daji, inda wani yaro matashi ya mutu bayan bam ya tashi da shi yayin da yake ƙoƙarin tserewa.
Tinubu ya umurci jami’an tsaro su gaggauta ceto gomman mutanen da aka sace a Neja
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya umarci rundunar soji, ’yan sanda, DSS da sauran hukumomin tsaro da leƙen asiri da su ƙaddamar da aikin ceto gomman mutanen da aka sace a wani hari a jihar Neja da ke tsakiyar ƙasar.
A wata sanarwa da shugaban ya fitar, ya bayyana takaicinsa kan sacewa da kashe wasu fararen hula da miyagu suka yi a jihar, inda ya ce waɗanda suka kai harin ba za su tsere wa hukunci ba.
“Waɗanda suka kai wannan mummunan hari kan ƴan Najeriya, maƙiyan zaman lafiya ne kuma maƙiyan bil’adama ne, kuma ba za su tsira daga hukunci ba," in ji Tinubu.
Tinubu ya ce gwamnati ba za ta huta ba har sai an dawo da ƴaƴa, iyaye da sauran mutanen da aka sace ga iyalansu lafiya.
Ya kuma umarci shugabannin hukumomin tsaro da su riƙa ba shi rahoto kan ci gaban aikin ceto har sai an gano duk mutanen da aka sace.
Tinubu ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya za ta ba gwamnatin jihar Neja dukkan goyon bayan da ake buƙata domin aikin ceto mutanen.
Amurka ta cire Syria daga jerin ƙasashe masu taimaka wa ta’addanci
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin
Amurka ta cire Syria daga jerin ƙasashe masu taimaka wa ta'addanci bayan shekara 47,
wani abu da a tsawon lokaci ya zama tarnaƙi mafi girma ga zuba jari a ƙasar
da kuma mayar da ita saniyar ware a hada-hadar tattalin arziƙin duniya.
Sakataren
harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya ce an ɗauki matakin ne bisa la’akari da
ƙoƙarin da ƙasar ta Syria ke yi wajen nesanta kanta daga ayyukan ta’addanci na
ƙasa da ƙasa.
Amurka
ta janyo sabon shugaban Syria Ahmed al-Sharaa a jiki, wanda ya kasance tsohon ɗan
yakin sunƙuru wanda a baya Amurka ta yi alƙawarin bayar da lada ga duk wanda ya
taimaka aka kama shi.
Haka
nan an cire ƙungiyar da ya jagoranta ta Hayat Tahrir al-Sham (HTS) daga jerin
ƙungiyoyin ta’addanci na duniya.
HTS
wadda a baya ake kira al-Nusra Front, ta kasance wani reshe na ƙungiyar al-Qaeda a
Syria har zuwa lokacin da Sharaa ya yanke hulɗa da ƙungiyoyin jihadi a 2016.
Mataimakin shugaban ƙasar Tanzaniya ya ajiye aiki
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Mataimakin shugaban ƙasar Tanzaniya Emmanuel John Nchimbi
Mataimakin shugaban ƙasar Tanzania Emmanuel Nchimbi ya sanar da ajiye aiki, inda ya ce ya fara shirye-shiryen yin ritaya daga harkokin siyasa.
A wata takarda da ya rubuta wa shugabar ƙasar Samia Suluhu Hassan, wadda ya wallafa a shafinsa na Instagram, Nchimbi ya ce ajiye aikin nasa zai fara ne daga ranar 4 ga watan Satumba.
Majiyoyi daga ofishin shugaban ƙasar da mataimakin shugaban sun tabbatar wa BBC batun ajiye aikin.
Ya zama mataimakin shugaban ƙasa na farko da ya ajiye aiki a ƙasar ta Tanzania tun bayan samun ƴancin ƙasar a shekarar 1964.
Ya ajiye aikin ne ƙasa da shekara ɗaya bayan rantsar da shi a muƙamin ranar 3 ga watan Nuwamba.
Nchimbi ne ya mara wa shugaba Samia Suluhu baya a zaɓen watan Oktoban 2025 wanda ke cike da rikici da zanga-zanga, lamarin da ya kai ga kashe sama da mutum 500.
Jam'iyyun adawa da ƙungiyoyin kare hakkin bil'adama sun zargi jami'an tsaro da yin amfani da ƙarfi fiye da kima kan masu zanga-zangar adawa da gwamnati.
A baya-bayan nan an samu rahotannin rashin jituwa tsakanin shugabar ƙasar da mataimakin nata.
Gwamnan Gombe bai isa ya yi min ritaya a siyasa ba - Sanata Goje
Asalin hoton, Muhammad Adamu Yayari/FB
Bayanan hoto, Sanata Danjuma Goje
Yayin da ake ci gaba da hasashen matakin da zai ɗauka bayan dambarwar da ta taso daga zaɓukan fitar da gwani na jam'iyyar APC, wadda ta kai ga ya sara tikitin takarar sanata, tsohon gwamnan jihar Gombe kuma sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya, Muhammed Ɗanjuma Goje ya ce zai ci gaba da mara wa jam'iyyar APC baya domin ta samu nasara a zaɓe mai zuwa.
A baya dai an yi hasashen cewa jigon a siyasar jihar Gombe da ke yankin Arewa maso gabashin Najeriya zai sauya sheƙa zuwa wata jam'iyya domin ƙalubalantar hana shi takara a APC duk da cewa shi ke kujerar a yanzu haka.
Sai dai a hirar shi da BBC, Sanata Goje ya ce ya ɗauki rashin samun tikitin nasa a APC a matsayin ƙaddarar rayuwa daga Allah, kuma ya gamsu cewa ya cimma duk matakin da ya kamata ya kai a siyasance domin haka lokaci ne ya zo na ''komawa gefe ya bari ƴan baya su shiga.''
Katafaren jirgin ruwan yaƙin Amurka zai je Thailand don hutawa
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Jirgin ruwan yaƙi na Amurka
Jirgin
ruwan dakon jiragen yaƙi na Amurka USS Abraham Lincoln zai isa tashar jiragen
ruwa a Thailand a mako mai zuwa bayan kwashe tsawon lokaci a cikin ruwan
teku a Gabas ta Tsakiya, in ji hukumomin Thailand.
Wannan
na zuwa ne bayan rahotannin nuna damuwa game da mummunan yanayin da sojojin da
ke cikin jirgin ke ciki, wanda ya hada da taɓarɓarewar lafiyar ƙwaƙwalwa da sauran
abubuwa.
Wani
ɗan majalisar dokokin Amurka na jam’iyyar Democrat ya ce jirgin ya kafa tarihin
kwashe sama da kwana 200 a kan teku ba tare da hutawa ba.
Jami’in
gwamnatin Thailand wanda bai so a bayyana sunansa ba ya ce kimanin sojoji da ma’aikatan
jirgin 5,000 za su isa Thailand inda za su huta, bayan shafe tsawon lokaci yana
aiki a teku.
Rundunar
sojin Thailand ba ta yi martani ba a lokacin da aka bukaci tsokacinta kan lamarin.
Ya kamata a yi wa Najeriya addu’a kan matsalar tsaro – Tinubu
Asalin hoton, PRESIDENCY NIGERIA
Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Bola Tinubu
Shugaban
Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci al’ummar ƙasar su dage wajen yin addu’o’in magance matsalar
tsaro da sauran bala’o’i da ƙasar ke fama da su.
A
cikin saƙon da ya fitar na ranar Maulidi ta hannun mai taimaka masa kan yaɗa labarai
Bayo Onanuga, Tinubu ya ce “ya kamata Musulmai su dage wajen yin koyi da
koyarwar Annabi Muhammad.
“Akwai
darussa masu kyau da za a koya daga ɗabi’un (Annabi Muhammad) na dagewa, juriya,
haƙuri da juna, ƙankan da kai da rashin nuna son kai,” in ji Tinubu.
Haka
nan shugaban ya buƙaci malaman addini a ƙasar su yi amfani da lokacin wajen yi
wa ƙasar addu’a tare da yi wa al’umma huɗubar koyi da Annabi Muhammad a al’amuransu
da suka jiɓanci kishin ƙasa.
A
ranar Litinin ne al’ummar Musulmi a faɗin duniya ke murnar ranar haihuwar Annabi
Muhammad.
Hakan
na zuwa ne yayin da Najeriya ke ci gaba da fuskantar matsaloli na tsaro da
tattalin arziƙi, yayin da alummar ƙasar ke kokawa kan tashin farashin man fetur da kayan masarufi waɗanda
suka ta’azzara tun bayan hawan Bola Tinubu mulki a shekarar 2023.
Gwamnatin Indiya za ta fitar da albasa daga rumbu don sassauto da farashi
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Firaiministan Indiya Narendra Modi
Gwamnatin ƙasar Indiya ta ce za ta fitar da albasar da ta jibge a rumbunanta a wani yunƙuri na sassauta farashin albasa da ya yi tashin gwauron zabi a ƙasar.
An saba cewa farashin albasa kan tashi a ƙasar Indiya cikin watan Agusta sanadiyyar yadda ake matuƙar buƙatar kayan-gwari domin bukuwa - to sai dai a wannan shekarar farashin ya kusa nunka yadda aka riƙa sayen ta a shekarar da ta gabata.
Gwamnati za ta yi amfani da jiragen ƙasa wajen jigilar albasar zuwa birane kamar Chennai da Kochi, kuma ta ce motoci za su riƙa zagayawa suna sayar da alabasar a unguwannin Delhi, babban birnin ƙasar.
An ga wani jirgin sojin Amurka ya sauka a Rasha
Asalin hoton, Getty Images
Fadar shugaban ƙasar Rasha ta ƙi cewa uffan game da rahotannin da ke cewa wani jirgin jigilar kaya na sojojin Amurka ya sauka a filin jirgi na Vnukovo da ke birnin Moscow.
Manhajar bibiyar zirga-zirgar jiragen sama ta FlightRadar ta nuna jirgin na barin sansanin sojin sama na Andrews Airbase da ke jihar Maryland a Amurka sannan ya sauka a Riga, babban birnin ƙasar Latvia, kwana biyu da suka gabata.
Akwai raɗe-radin da ke yawo a kafafen yaɗa labarai na Rasha cewa ko dai za a yi musayar fursunoni ne ko kuma watakila jirgin ya kai jakadan shugaba Donald Trump ne domin tattaunawa kan Ukraine.
A baya akwai rahotannin da ke cewa jakadan Trump, Steve Witkoff da Jared Kushner za su iya halartar bikin ranar ƴanci ranar Litinin a birnin Kyiv, sai dai ba a ga hakan ba.
Isra'ila na ci gaba da kashe mutane a Gaza - MDD
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa hare-haren Isra'ila na ci gaba da kashe fararen hula a Gaza.
Ma'aikatan lafiya a yankin sun ce an kashe wata yarinya ƴar shekara 10 da kuma wani yaro ɗan shekara huɗu a cikin kwana ɗaya da ya gabata.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ba ta da masaniya game da kisan yarinyar, inda ma'aikatan lafiya da dangi suka ce harsashin bindiga ya samu Amal Abu Khater a baya sa'ilin da take zaune tana cin abinci a cikin tantin da take zama da iyalanta a Khan Younis.
Ofishin bayar da agajin jin-ƙai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce hare-haren Isra'ila sun lalata rumbunan ajiye kaya guda uku mallakinsa a garin Deir al-Balah.
'Yadda Annabi ke kyautata wa yara shi ya sa nake son Maulidi'
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Yayin da ake murnar Maulidin Annabi Muhammadu (SAW), wata budurwa a Kano, Zainab Sanusi ta bayyana mana shirye-shiryen da take yi na murnar ranar.
Ta yaya za ku yi murnar wannan rana?
An kama tsohuwa ƴar shekara 101 da zargin sayar da wiwi
Asalin hoton, NDLEA/FB
An
kama wata tsohuwa wadda hukumomi suka ce shekarunta 101 a Najeriya bisa zargin
sayar da tabar wiwi, wani abu da ya ja hankalin al’umma.
A
ranar Asabar ne Hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce ta kama
Esther Ogunmabo, wadda aka ce tana da jikoki, a jihar Ogun da ke kudu maso
yammacin Najeriya.
Mai
magana da yawun hukumar Femi Babafemi ya ce an kama matar ne da “ƙulli-ƙullin wiwi wadda ta kai nauyin giram 90, inda ta ce tana sayarwa ne ga mutunen unguwa”.
NDLEA
ta ce matar ta ce ta shiga harkar sayar da ganye ne bayan gobarar da ta lalata
shagonta na kayan masarufi. Amma an bayar da belin ta.
Hukumar
ta ce wata ƴar tsohuwar ce da ke zaune a birnin Legas ake zargi da tura mata
tabar bayan kwana hurhuɗu, inda ita kuma tsohuwar ake zargin tana sayar wa
mutane kulli-ƙulli a cikin unguwa.
An buƙaci mutanen Tigray su yi bikin Maulidi a cikin gida
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wani mai bikin Maulidi a birnin Addis Ababa na ƙasar Ethiopia
Majalisar kula da lamurran addinin Musulunci ta yankin Tigray a ƙasar Ethiopia ta buƙaci
Musulman yankin su yi bukukuwan maulidi a cikin gida ko ɗakunan taro, sannan
kada su je masallatai sai cikin dare domin gudun hare-hare daga sojojin ƙasar.
“Majalisar
ta ce ba za a yi bukin Maulidi a manyan dandalin taruka ba, a maimakon haka za
a gudanar da maulidin ne a masallatai, inda za a yi addu’o’i da wa’azi,” a
cewar bayanin.
Al’ummar
Ethiopia na hutu a yau Talata domin bikin maulidin haihuwar Annabi Muhammad,
wanda ke gudana a ƙasashe da dama na duniya.
Majalisar
addinin Musuluncin ta yankin Tigray ta ce za a yi bukukuwan na masallatai ne a
cikin dare domin gudun hare-haren jirage marasa matuƙa na sojojin gwamnati.
Ana
samun rahotannin hare-haren jirage marasa matuƙa a yankin Tigray daga sojojin
gwamnatin Habasha, inda irin waɗannan hare-hare suka faɗa birnin Makelle da
wasu sassan yankin, lamarin da ke haifar da asarar rayuka da raunata fararen
hula.
An
samu irin wannan hari a ranar 18 ga watan Agusta a birnin na Makelle.
Ethiopia
ta dade tana yaƙi da mayaƙan ƙungiyar ƴanta al’ummar Tigray ta TPFL, lamarin da
ya haifar da asarar ɗimbin rayuka da tarwatsa mutane daga muhallansu.
Dakarun Amurka sun fara horas da na Najeriya a Bauchi
Asalin hoton, Africom
Dakarun Amurka sun fara horas da twakwarorinsu na Najeriya kan yadda ake sarrafa jirage marasa matuƙa da kuma kula da sojojin da suka samu rauni a lokacin yaƙi a wani ɓangare na alaƙar tsaro da ƙasashen biyu suka ƙulla.
Rahoton na Africom ya ce horon ya mayar da hankali kan sarrafa jirage marasa matuƙa, sarrafa makamai, cire bama-bamai, kula da waɗanda suka ji rauni da kuma dabarun yaƙi ga ƙaramar tawagar soji.
"Amurka da Najeriya na gudanar da aikin bayar da horo a sansanin horon soji da ke a Bauchi, Najeriya, bisa manufar musayar ƙwarewa, ƙarfafa abokan hulɗa da kuma yauƙaƙa alaƙa tsakanin ɓangarorin biyu," a cewar bayanin.
Horon na zuwa ne bayan a watan Yuli Amurka ta sanar da janye akasarin dakarunta da ta tura Najeriya domin wani aikin yaƙi da ta'addanci na musamman, yayin da ƙasashen biyu suka ci gaba da shirinsu na musayar bayanan sirri da tsaro.
A ƙarshen shekarar 2025 ne ƙasashen biyu suka ƙulla wata alaƙa ta tsaro bayan shugaban Amurka Donald Trump ya yi zargin cewa ana gallaza wa Kiristoci a Najeriya tare da matsa wa hukumomin Najeriyar lamba kan su magance matsalar tsaro.
An samu nasara a tattaunawar sulhu da Iran - Pakistan
Asalin hoton, IRNA
Bayanan hoto, Shugaban hafsoshin sojin Pakistan Asim Munir ya gana da shugaban Iran Masoud Pezhakian a Tehran
Pakistan ta ce an samu gagarumar nasara a tattaunawar da wakilanta suka yi da shugabannin Iran a Tehran, wadda ta mayar da hankali kan hanyoyin samar da zaman lafiya.
Shugaban hafsoshin sojin Pakistan, Field Marshal Asim Munir, ne ya jagoranci tawagar kasar a ziyarar.
Rahotanni sun ce tattaunawar da ya yi da shugaban Iran da ministan harkokin wajen kasar da kuma shugaban majalisar dokoki ta mayar da hankali ne kan matakan dakile ci gaba da rikicin, da sake bude Mashigar Hormuz, da kuma neman hanyoyin kawo karshen yaƙin da ake yi tsakanin Iran din da Amurka.
An kuma ruwaito cewa Field Marshal Munir ya tuntuɓi Shugaban Amurka, Donald Trump, kafin tafiyarsa Tehran.
Rahotanni sun ce Amurka ta nemi Pakistan ta yi amfani da tasirinta wajen shawo kan Iran ta koma teburin tattaunawa.
Sai dai kawo yanzu babu wata sanarwa daga Washington game da sakamakon ganawar.
Iran ta mayar wa da Amurka martani da cewa, Amurkar ta daɗe ba ta tsaurara mata takunkumin tattalin arziƙin da take mata barazana da shi ba, tana mai cewa tana da ƙwarin gwiwa cewa abokan hulɗar kasuwancinta za su bijire wa duk wani matsin lamba daga Washington.
Ministan kudin Iran, Ali Madanizadeh, ya ce takunkumi ba sabon abu ba ne ga ƙasarsa.
Ya ce, idan maƙiyan ƙasar suka ƙaddamar da abin da ya kira "ta'addancin tattalin arziƙi", Iran ma tana da nata hanyoyin mayar da martani kuma ta san yadda ake takun-saƙar - ba layance mata za a yi ba.
Shugaban majalisar ƙoli ta tsaron Iran, Mohsen Rezaei, ya yi gargaɗin cewa Tehran a shirye take ta dakatar da dukkan fitar da man fetur daga ƙasashen yankin Tekun Fasha.
A jiya Litinin Sakataren Baitulmalin Amurka, Scott Bessent, ya ce bankuna da kamfanoni da kuma ƙasashen da suka ci gaba da hulɗa da Iran za su fuskanci irin yadda ake mayar da Iran saniyar-ware a fannin tattalin arziƙi, idan suka ki katse dangantakarsu da ita.
Barka da Maulidi!
Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata a wannan shafi na BBC Hausa, inda muke kawo muku muhimman labarai kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a Najeriya, maƙwaftanta da kuma sassan duniya.
Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook, instagram da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.